'Yan Bindiga Sun Farmaki Ayarin Dan Takarar Gwamnan SDP a Jihar Kogi

'Yan Bindiga Sun Farmaki Ayarin Dan Takarar Gwamnan SDP a Jihar Kogi

  • Miyagun 'yan bindiga da ake zargin 'yan daban siyasa ne sun farmaki ayarin ɗan takarar gwamnan SDP a jihar Kogi
  • Rahoto ya bayyana cewa maharan sun kai wannan hari ne yayin da Yakubu Ajaka da jiga-jigan SDP ke hanyar dawowa daga wurin taro
  • Hukumar 'yan sandan jihar ta ce tuni ta fara bincike kan harin kuma an kama ASP da ake zargi da hannu a lamarin

Jihar Kogi - Wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan ayarin motocin Murtala Yakubu-Ajaka, dan takarar gwamna na jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) a jihar Kogi.

Lamarin ya faru ne a ranar Laraba lokacin da Ajaka da wasu jiga-jigan SDP ke dawowa daga taron masu ruwa da tsaki a yankin Ogori Magongo.

Dan takarar gwamna a inuwar jam'iyyar SDP, Murtala Yakubu-Ajaka.
Yan bindiga sun farmaki ayarin ɗan takarar gwamna a jihar Kogi Hoto: Murtala Yakubu-Ajaka
Asali: UGC

Rahoton The Cable ya tattaro cewa ‘yan bindigan sun yi artabu da jami’an tsaro a wata musayar wuta kafin daga bisani su bar motocinsu guda biyu su gudu.

Kara karanta wannan

Zaben Gamnan Kogi: Tashin Hankali Yayin da Magoya Bayan APC Da SDP Suka Yi Musayar Wuta

Bayan harin, an kama wani mataimakin Sufuritandan ‘yan sanda (ASP) bisa zarginsa da jagorantar ‘yan barandan da suka kai harin a jihar Kogi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin wani faifan bidiyo, an ga dan sandan wanda jikinsa ya gaya masa, ana yi masa tambayoyi.

Mun fara bincike kan lamarin - yan sanda

A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, William Aya, kakakin rundunar ‘yan sandan Kogi, ya ce rundunar ta fara gudanar da bincike kan bidiyon.

Aya ya ce rundunar ‘yan sandan jihar Kogi ta kuduri aniyar samar da daidaito ga dukkanin jam’iyyun siyasa, kamar yadda Guardian ta ruwaito.

A kalamansa, kakakin 'yan sandan ya ce:

"Yayin da ya ke yin Allah wadai da lamarin Kwamishinan ƴan sanda ya ce an dora wa mataimakin kwamishinan ‘yan sandan da ke kula da sashen binciken manyan laifuka alhakin fara bincike."

Kara karanta wannan

Muhimman Abubuwa 5 Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Sabuwar Rundunar Tsaro Ta Jihar Katsina

"CP ya sake nanata kudurin rundunar na ci gaba da zama da masu ruwa da tsaki a harkokin tsaron zabe domin tabbatar da ingantaccen muhalli da tsaro yayin gudanar da zabe."

'Yan Bindiga Sun Farmaki Gidan Yari a Jihar Cross River, Sun Harbe Mai Gadi

A wani rahoton kuma Wasu mahara da ake kyautata zaton mayaƙa ne sun kai sabon hari kan gidan gyaran hali a jihar Kuros Riba.

Wasu majiyoyi sun bayyana cewa maharan sun bindige jami'i ɗaya har lahira sun kuma tafi da bindigarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel