Kwankwaso Ya Ba da Gudunmawar Gida Don Inganta Ilimin Almajirai a Jihar Kano

Kwankwaso Ya Ba da Gudunmawar Gida Don Inganta Ilimin Almajirai a Jihar Kano

  • Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso ya kaddamar da wata hukuma da za ta inganta harkar ilimin almajirai
  • Sanatan ya bayyana cewa hukumar za ta dauki mahaddata Alkur’ani don ba su horaswa na musamman da binciken Musulunci
  • Gwamna Abba Kabir ana shi jawabin, ya godewa tsohon gwamnan inda ya ce hakan zai inganta harkar ilimi a jihar

Jihar Kano – Sanata Rabiu Kwakwaso ya kaddamar da Hukuma da za ta inganta karatun addinin Musulunci da bincike don inganta ilimin zamani ga almajirai.

Hukumar mai suna Majidadi za ta inganta rayuwar almajirai da kuma rage yawan barace-barace a cikin al’umma.

Kwankwaso ya kaddamar da hukumar kula da almajirai a Kano
Kwankwaso ya yi alkawarin ci gaba da inganta ilimin almajirai. Hoto: Rabiu Kwankwaso.
Asali: UGC

Wane gudumawa Kwankwaso ya bayar ga Musulunci?

Kwankwanso ya kaddamar da hakan yayin da ya ke cika shekaru 67 a duniya inda ya ce hukumar za ta yi wa almajirai da su ka haddace Alkur’ani horo na musamman da satifiket na makarantar boko.

Kara karanta wannan

Ministan Abuja Ya Sake Dauko Gingimemen Aiki, Da Yiwuwar Ya Kwace Wasu Gidaje a FCT

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce ba wai rage ma su bara kadai ba a tituna, hukumar za ta samar da hanyoyin bunkasa rayuwarsu musamman ga ma su barar, Daily Trust ta tattaro.

A cewarsa:

“Za su samu horaswa na musamman a yarukan Turanci da kuma Larabci yayin da za su yi amfani da satifiket din don karin karatu.
“Hukumar za kuma ta ba da kofa ga wadanda su ka haddace Alkur’ani musamman wadanda su ka dace don ba su ilimi ingantacce.”

Ya kara da cewa hukumar wanda ke gidansa da ke hanyar Miller za ta ba da kofa ga kowa ba tare da nuna bambanci ba a cikin al’umma, cewar Tribune.

Daga cikin tsare-tsaren hukumar akwai ba da horaswa na musamman wanda za a ba da satifiket na firamare da sakandare har ma da na Difloma.

Kara karanta wannan

Tsautsayi: Kwantena Mai Tsayin 40 Ta Faɗo Daga Bayan Tirela, Ta Murƙushe Wata Mata Har Lahira

Kwankwaso ya ce hakan zai ba su damar samun damar neman gurbin karatu a Jami’o’i don inganta rayuwarsu.

A martaninshi, Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya yabawa sanatan inda ya ce hakan zai kara inganta harkar ilimi a jihar.

Ya yi alkwarin gyara tsangayoyi 44 da ke kananan hukumomin jihar da kuma samar da kayayyakin karatu don kara musu karfin gwiwa.

Abba Kabir ya dauki nauyin dlibai 1001 zuwa kasashen waje

Kun ji cewa Gwamna Abba Kabir ya dauki nauyin dalibai guda 1001 zuwa kasashen Indiya da Uganda don karo karatu.

A jiya Juma’a ne gwamnatin ta fara da kason farko dalibai 550 zuwa kasar Indiya don karo karatun digiri na biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.