Abun Bakin Ciki
Ƴar tsohon gwamnan jihar Oyo, Chief Omololu Olunloyo, Kemi Olunloyo ta barranta kanta da iyalanta inda ta ce ta fita daga cikin dangin Olunloyo baki daya.
Rahotanni sun tabbatar da rasuwar babban jigon jam'iyyar APGA, Maja Umeh ranar Laraba, 9 ga watan Afrilu, 2025, ya mutu yana da shekara 64 a duniya.
Wani sufeton ƴan sanda ya rasa rayuwarsa a gidan kallon kwallo ana tsak da wasan Arsenal da Real Madrid a Kalaba, babban birnin jihar Kuros Riba.
Bayan sanar da rasuwar dan majalisa a Zamfara, Hon. Aminu Ibrahim Kasuwar Daji, Sanata Yau Sahabi ya nuna alhini kan rasuwar marigayin inda ya ce bawan Allah ne.
Gobarar kasuwar Zamfara ta kone shaguna 55, inda ta shafi sashen masu sayar da magungunan gargajiya. 'Yan kasuwa sun roƙi gwamnati ta kai masu dauki.
Shugaban kamfanin MTN na farko kuma attajirin ɗan kasuwa da ya kafa bankin Diamond, Pascal Gabriel Dozie ya kwanta dama, mun haɗa maku abubuwan sani gane da shi.
Hatsarin mota ya yi ajalin wasu fitattun mawaƙan ikilisiyya su 4 a jihar Ogun, hukumar kiyaye haɗurra watau FRSC ta bayyana cewa hatsarin ya auku ne sabida gudu.
Babbar kotu da ke zamanta a Jos din jihar Plateau ta dage shari’ar kisan gilla kan Manjo-Janar Idris Alkali zuwa 28 da 29 ga watan Mayun shekarar 2025.
Babban malamin Izala, Imam Bello Jandutsi ya rasu a Birnin Kebbi bayan shekaru 30 yana limanci da da’awa. Za a yi jana’izarsa a masallacin Sheikh Abbas, Rafin Atiku.
Abun Bakin Ciki
Samu kari