Zance Ya Kare: Sheikh Daurawa Ya Yi Magana kan Dan Takarar da Zai Yi Wa Kamfe a 2027

Zance Ya Kare: Sheikh Daurawa Ya Yi Magana kan Dan Takarar da Zai Yi Wa Kamfe a 2027

  • Kwamandan hukumar Hisbah ta Jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya ce shi ba ɗan siyasa ba ne kuma ba zai yi wa wani ɗan siyasa kamfen ba
  • An saka sunan Daurawa da tsohon shugaban hukumar NAHCON, Sheikh Abdullahi Saleh Pakistan, cikin kwamitin yaƙin neman zaɓen APC a Kano
  • Malamin ya ce yana fatan Allah ya ba da nasara ga duk wanda zai tabbatar da adalci, tausaya wa talakawa da inganta rayuwarsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Babban Kwamandan Janar na Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya bayyana matsayarsa kan yi wa wani dan takara kamfe gabanin zaben 2027.

Sheikh Aminu Daurawa ya bayyana cewa shi ba ɗan siyasa ba ne kuma ba zai yi wa wani ɗan siyasa kamfen ba gabanin babban zaɓen shekara mai zuwa ba.

Kara karanta wannan

Tirkashi: An yanke wa mutumin da ya kashe abokinsa kan tashi sallar Asubah hukunci a Kano

Daurawa.
Babban kwamandan Hisbah na jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa Hoto: Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa
Source: Facebook

Yadda aka sa Daurawa a kwamitin kamfe

Daily Trust ta ruwaito cewa an saka sunan malamin kwamitin ba da shawara kan yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da na gwamna na APC a Kano.

Bayan Daurawa, an ga sunan tsohon shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Najeriya (NAHCON), Sheikh Abdullahi Saleh Pakistan, da wasu malaman addini cikin jerin mambobin kwamitin kamfen.

Malaman biyu sun fuskanci suka bayan shugaban APC na jihar, Hon. Umar Haruna Doguwa, ya fitar da jerin sunayen mambobin kwamitin, inda mutane da dama suka nuna rashin amincewarsu da saka su a ciki.

Sheikh Daurawa ya fadi matsayarsa

Sai dai a wani saƙo da ya wallafa da harshen Hausa a shafinsa na Facebook ranar Asabar, Daurawa ya ce yana fatan samun nasara ga duk wanda zai tabbatar da adalci, tausaya wa talakawa da kuma inganta rayuwarsu.

Daurawa ya ce:

“Ni ba ɗan siyasa ba ne, kuma ba zan yi wa kowa kamfen ba. Sai dai ina fatan duk wanda zai tabbatar da adalci, ya tausaya wa talakawa, ya kare haƙƙoƙinsu kuma ya yi aiki don inganta rayuwarsu, Allah Ya ba shi nasara.

Kara karanta wannan

Na kusa da Ganduje ya yi tsiya, ya yi murabus daga jam'iyyar APC a Kano

“Allah Ya ba mu shugabanni masu gaskiya, amana da tsoronSa, waɗanda za su fifita muradun jama’a a kan muradunsu na kansu. Amin, Ya Rabbal Alamin.”
Daurawa.
Babban kwamandan rundunar Hisbah ta Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa Hoto: Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa
Source: Facebook

Duk da cewa Daurawa bai yi magana kai tsaye kan saka sunansa cikin kwamitin ba da shawara na kamfen ɗin APC ba, bayanin nasa ya zo ne a daidai lokacin da ake sukar shigar malaman addini cikin harkokin siyasar jam’iyyu gabanin zaɓen 2027.

Ana ganin wannan sako da ya fitar ya kara tabbatar da cewa malamin ba zai yi wa jam'iyyar APC mai mulki yakin neman zabe ba.

Daurawa ya yi magana kan siyasar Najeriya

A wani labarin, kun ji cewa Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya yi magana game da rikicin siyasa da ya taso musamman kan tikitin Musulmi da Musulmi.

Daurawa ya ce siyasa ba addini ba ce, yana mai cewa bai kamata a hada rigingimun addini da siyasar Najeriya ba

Malamin ya bayyana cewa ya kamata ’yan Najeriya su zabi shugabanni bisa kwarewa, ayyukan alheri da abin da suke tsammanin za su yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262