Da Gaske An Fitar da Naira Tiriliyan 2.3 don Kaddamar da Kamfen APC a Kaduna? Gaskiya Ta Fito
- Gwamnatin Jihar Kaduna ta bayyana zargin cewa Gwamna Uba Sani ya fitar da Naira tiriliyan 2.3 don ƙaddamar da kamfen APC a matsayin ƙarya
- Kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Ahmed Maiyaki, ya ce babu wani kuɗi da suka kai wannan adadi da aka ware
- Gwamnatin ta yi kira ga hukumomin tsaro da na bincike su gano waɗanda suka ƙirƙiri wasiƙar, tare da ɗaukar matakin shari’a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kaduna, Nigeria - Gwamnatin Jihar Kaduna ta musanta wata wasiƙa da ke yawo a intanet, wadda ke zargin Gwamna Uba Sani da sakin Naira tiriliyan 2.3 domin ƙaddamar da kamfen shugaban ƙasa na APC.
Gwamnatin ta ce wasiƙar ta bogi ce kuma mai ruɗarwa, inda ta zargi waɗanda suka ƙirƙire ta da ƙoƙarin ɓata sunan gwamnan, wanda ta ce ya shahara wajen bin ƙa’idojin tafiyar da kuɗaɗen gwamnati da gudanar da mulki cikin gaskiya.

Source: Facebook
Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu na jihar, Malam Ahmed Maiyaki, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a Kaduna, kamar yadda Vanguard ta
Gwamnatin Kaduna ta yi bayani
Maiyaki ya ce wasiƙar, mai ɗauke da kwanan wata 18 ga Oktoba, 2026, mai taken “Sanarwa kan Shirye-shiryen Babban Taron Ƙaddamar da Kamfen”, tana ɗauke da kura-kurai da suka sanya shakku kan sahihancinta.
Ya ce wasiƙar, wadda ake zargin an aika wa Sanata Abdulazeez Yari, darakta-janar na kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC, ta yi iƙirarin ƙarya cewa an saki Naira tiriliyan 2.3 domin ƙaddamar da kamfen ɗin.
Kwamishinan ya nuna cewa kasafin kuɗin Jihar Kaduna na 2026 ya kai Naira biliyan 985.92, wanda ke nufin adadin kuɗin da aka yi zargin an kashe ya ninka kasafin kuɗin jihar na shekara fiye da sau biyu.
Ya ce wannan iƙirari ba shi da tushe ta fuskar alkaluman kuɗin Kaduna, kuma babu wani ingantaccen kundin kasafi, amincewa ko bayanan kashe kuɗi da ke tabbatar da shi.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Tinubu ta ɗauko hanyar gyara, za a samu rangwamen tsadar rayuwar kwana 90
An gano kura-kurai a takardar
Maiyaki ya kuma nuna wasu kura-kurai a wasiƙar, ciki har da rubuta sunan gwamnan ba daidai ba a matsayin “Uba Sai” da kuma alamun cewa an yi amfani da sa hannunsa ba tare da izini ba.
“Gwamnatin Jihar Kaduna ta fito fili ta nesanta kanta daga wannan takarda. Gwamna Uba Sani bai rubuta wasiƙar da ake magana a kai ba, kuma bai ba da izinin rubuta ta ba. Ba a ware, amincewa ko sakin Naira tiriliyan 2.3 ba,” in ji shi.

Source: Facebook
Ya bayyana zargin a matsayin ƙirƙirarren labari da kuma yunƙurin yaudarar jama’a da gangan, kamar yadda Tribune Nigeria ta ruwaito.
Jami'an tsaro na ganin fastocin Tinubu
Kun ji cewa an ga jami’an tsaro suna gadin fastoci da allunan tallata Shugaban Ƙasa Bola Tinubu a birnin Kaduna yayin da ake shirin kaddamar da kamfe.
Jami'an tsaron sun mamaye wurare daban-daban musamman a manyan hanyoyin da suka doshi filin wasa na Kaduna Township Stadium, inda ake sa ran gudanar da gangamin.
Asali: Legit.ng
