Hukumomin Amurka Sun Magantu da Aka Yi Kisa a Bakin Masallaci da Musulmi Ke Salla
- Wani mutum ya mutu, yayin da wani ya jikkata sakamakon harbin bindiga da ya faru kusa da wani masallaci
- Rundunar ’yan sandan Columbus ta ce harbin bai shafi masallacin ba, illa dai ya biyo bayan wata takaddama da ta faru
- ’Yan sanda sun tabbatar da mutuwar mutum guda, amma ba su bayyana halin da wanda ya jikkata yake ciki ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ohio, US - Wani mutum ya mutu, yayin da wani ya jikkata bayan an yi harbin bindiga kusa da wani masallaci da ke arewa maso gabashin birnin Columbus, jihar Ohio ta Amurka.
Rundunar ’yan sandan Columbus ta ce ta samu kiran waya da dama da ke ba da rahoton karar harbe-harbe da misalin ƙarfe 2:11 na rana, a yankin titin Albert Avenue mai lamba 2200.

Source: Twitter
Sashen ofishin kula da makamai, taba, barasa da abubuwan fashewa na Amurka (ATF) a Columbus ya ce jami’ansa na amsa rahoton harbin bindiga a wani masallaci da ke yankin, cewar Al Jazeera.
Sai dai ’yan sandan Columbus sun bayyana cewa ba masallacin aka nufa da harin ba, domin harbin ya biyo bayan wata takaddama a wani rukunin gidajen haya da ke kusa.
An harbe mutum guda har lahira a ranar Litinin da rana, yayin da aka gano wani mutum da ya jikkata. Sai dai hukumomi ba su bayyana halin da wanda ya jikkatan yake ciki ba.
A cewar jami’in ’yan sanda, harbin ya faru ne a kusa da masallacin a lokacin da ake gudanar da wani taro a wurin.
Sajan James Fuqua na rundunar ’yan sandan Columbus ya ce:
“Muna son mu fayyace cewa wannan ba hari ne kan masallacin ba.”

Source: Getty Images
An rasa ran mutum 1 a harin

Kara karanta wannan
Kaico: Mutane da dama sun mutu yayin da suka je ɗibar ganima jikin wata tankar fetur
Jami'in ya tabbatar da cewa, abin takaici, mutum guda ya mutu sakamakon harbin wanda ya jefa jama'ar da ke kusa da yankin.
Tun da farko a ranar Litinin, hukumar ATF ta wallafa saƙo a shafinta na X cewa jami’anta na amsa rahoton harbin bindiga a masallacin, wanda ke arewa maso gabashin tsakiyar birnin Columbus.
Yankin ya ƙunshi rukunin gidajen haya masu hawa biyu da dama, baya ga masallacin, kamar yadda Arab News ta ruwaito.
Har zuwa lokacin fitar da rahoton, ’yan sanda, jami’an yankin da kuma mahukuntan masallacin ba su amsa saƙonnin waya da aka aika musu domin neman ƙarin bayani ba.
An rasa rayuka a harin masallacin Amurka
A baya, kun ji cewa mutane uku sun mutu bayan wani harin bindiga da aka kai masallacin cibiyar addinin Musulunci ta San Diego da ke California a Amurka.
Jami’an tsaro sun ce ana binciken harin a matsayin 'harin kiyayya ga Musulmai', yayin da wadanda ake zargi - wasu su biyu suka sheke kansu.
Wani jami’in tsaron masallacin mai suna Amin Abdullah ya rasa ransa yayin da yake kokarin kare jama’a daga harsasan 'yan bindigar.
Asali: Legit.ng
