Majalisar dokokin tarayya
Tajuddeen Abbas ya yi bayanin abin da ya sa Arewa maso Yamma ta samu Shugaban majalisar wakilai da mataimakin shugaban majalisar dattawa a lissafinsu na APC.
‘Yan adawa sun dunkule a wuri guda domin ganin sun samu galaba a majalisa, amma rashin hadin-kan jam’iyya mai rinjaye zai iya jawo ‘yan adawa su yi masu kafa
Sanatocin Ibo ba su yarda da ‘Dan takaran Tinubu ba a takarar Majalisa. An yi kira ga Bola Tinubu ya yi adalci, a tabbata Ibo ya zama shugaban majalisar dattawa
A makon jiya wani sabon Sanata ya rubutawa APC takarda, ya ce zai nemi shugabancin Majalisa. Patrick Ndubueze ya sanar da shugabannin NWC zai nemi shugabanci.
Da alama Tajudeen Abbas ya samu goyon bayan Bola Tinubu a tseren majalisa. ‘Dan majalisar na mazabar Zaria da kewaye yana da jan aiki a gabansa a takarar bana.
Musa Saidu ya ce Dattawan Arewa ba su tare da Godswill Akpabio domin Sanatan ba masoyin Arewa ba ne, hakan na zuwa ne bayan an ji wasu ‘Yan Arewa su na bayansa.
Rahotanni sun tabbatar da zaɓar Abbas Tajudeen da Benjamin Kalu, a matsayin shugabannin majalisar wakilai ta 10, na shirin kawo rikici a APC, an yi Allah wadai.
Tsohon Gwamnan Zamfara zai hada-kai da Sanatocin PDP domin yakar APC. Abdul’Aziz Yari ba zai janye takarar da yake ni na shugabancin majalisar dattawa a bana ba
Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi ya ce ya hakura da kudirinsa na son zama shugaban majalisar dattawa sannan ya marawa Godswill Akpabio, tsohon minista baya.
Majalisar dokokin tarayya
Samu kari