Rigima Sabuwa: Hadimin Tinubu Ya Yi Babban Zargi kan Kwankwaso

Rigima Sabuwa: Hadimin Tinubu Ya Yi Babban Zargi kan Kwankwaso

  • Bayo Onanuga ya zargi tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso, da ƙarfafa magoya bayansa su ƙera makamai gabanin babban zaɓen 2027
  • Onanuga ya yi zargin ne bayan wani jawabin da Kwankwaso ya gabatar a taron gangamin siyasa a Bichi, Jihar Kano
  • Mai fafutukar kare haƙƙin bil’adama, Musa Bala Gaye, ya buƙaci jami’an tsaro su shiga tsakani domin kare zaman lafiya a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Mai ba Shugaba Bola Tinubu shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ya yi zargi kan madugun Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Bayo Onanuga ya zargi tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso, da ƙarfafa magoya bayansa su shirya makamai gabanin babban zaɓen 2027.

Onanuga ya zargi Kwankwaso da shirin tayar da rikici
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Bayo Onanuga Hoto: Hon. Saifullahi Hassan, EFCC Nigeria
Source: Facebook

Onanuga ya yi wannan zargi ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X ranar Litinin, 16 ga watan Nuwamban 2027 bayan jawabin da Kwankwaso ya gabatar a wani gangamin siyasa a Bichi, Jihar Kano, ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta fadi karyar da ta ce an shirya kan kai wa Kwankwaso hari

Abin da Onanuga ya ce Kwankwaso ya faɗa

A cewar Onanuga, Kwankwaso ya faɗa wa magoya bayansa cewa: “Ku ci gaba da kasancewa cikin shiri; kada ku sassauta wa waɗannan marasa kunya.”

Mai ba shugaban ƙasa shawara ya kuma yi zargin cewa tsohon gwamnan ya ƙarfafa magoya bayansa su ƙera makamai masu haɗari.

Onanuga ya bayyana kalaman da ake dangantawa da Kwankwaso a matsayin abin damuwa, musamman yayin da ake shirin tunkarar zaɓen 2027.

Ya ce ya kamata shugabannin siyasa su yi amfani da matsayinsu wajen ƙarfafa haƙuri, juriya da zaman lafiya, maimakon furta kalaman da za a iya fassara su a matsayin kira ga magoya baya su yi arangama.

Onanuga ya kuma yi gargaɗin cewa Kano jiha ce mai tsananin zafin siyasa, don haka kalaman da za su iya tayar da hankali na iya ƙara tsananta rashin jituwa tsakanin magoya bayan jam’iyyun siyasa.

Mai kare haƙƙin bil’adama ya yi magana

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Kwankwaso ya fito ya gayawa duniya wani halin Peter Obi

Da yake mayar da martani kan zargin, wani mai fafutukar kare haƙƙin bil’adama, Comrade Musa Bala Gaye, ya buƙaci jami’an tsaro su shiga tsakani domin magance abin da ya kira barazana ga zaman lafiyar jihar, cewar rahoton Vanguard.

Gaye ya ce ana sa ran zaɓen 2027 zai kasance da gasa mai zafi tsakanin ’yan siyasa, amma ya kamata kamfen ya mayar da hankali kan manufofi, dabarun gudanar da mulki da kuma hanyoyin magance matsalolin al’umma.

Ya kuma nuna damuwa kan nauyin da ke wuyan shugabannin siyasa na hana daba da kuma kare mazauna jihar daga yiwuwar rikici tsakanin magoya bayan jam’iyyun da ke hamayya.

Kira ga shugabannin siyasa

Mai fafutukar ya jaddada cewa bambancin ra’ayin siyasa wani ɓangare ne na dimokuraɗiyya, amma ƙarfafa magoya baya su ƙera makamai masu haɗari zai iya kawo cikas ga gudanar da harkokin siyasa cikin lumana.

Ya buƙaci shugabannin siyasa su fito fili su fayyace kalaman da suka jawo ce-ce-ku-ce, tare da nuna jajircewarsu wajen gudanar da kamfen ba tare da tashin hankali ba.

Zarge-zargen sun sake jawo hankalin jama’a kan muhimmancin taka-tsantsan yayin shirya magoya baya da gangamin siyasa gabanin babban zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Tsaro ko tazarcen Tinubu: Matawalle ya bayyana babban burinsa a 2027

Onanuga ya yi zargi kan Kwankwaso
Hadimin Shugaba Bola Tinubu, Bayo Onanuga Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

'Yan daba sun farmaki tawagar Kwankwaso

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu da ake zargin ’yan daba ne sun kai hari kan ayarin motocin tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso.

An auka wa tawagar madugun na Kwankwasiyya ne tare da ɗan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar NDC, Aminu Abdussalam Gwarzo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng