Daga Karshe Manyan Arewa Sun Gabatarwa Tinubu Bukatarsu a Majalisa Ta 10

Daga Karshe Manyan Arewa Sun Gabatarwa Tinubu Bukatarsu a Majalisa Ta 10

  • Manyan arewa daga jihohi 19 sun zauna a Kaduna ranar Jumu'a, sun cimma matsaya kan shugabancin majalisa
  • A cewarsa duba da gudummuwar da arewa ta baiwa Tinubu, ita ya dace ta mulki majalisar tarayya ta 10
  • Wannan nan zuwa yayin da ake taƙaddama kan yadda jam'iyyar APC ta raba kujerun majalisa

Kaduna -Manyan arewa daga dukkan shiyyoyi sun haɗa baki, sun buƙaci zababben shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya saka wa arewacin Najeriya da kujerun shugabannin majalisa ta 10.

Sun kafa hujjar cewa shugaban ƙasa mai jiran gado da kuma Alƙalin alkalan Najeriya (CJN), Mai shari'a Olukayode Ariwoola, duk daga kudancin Najeriya suka fito.

NASS.
Daga Karshe Manyan Arewa Sun Gabatarwa Tinubu Bukatarsu a Majalisa Ta 10 Hoto: channelstv
Asali: Twitter

Jagororin da suka cimma wannan matsaya sun kunshi wakilan jihohin arewacin Najeriya 19 kuma daga bangarorin ilimi da siyasa, kamar yadda Channels tv ta rahoto.

Kara karanta wannan

Tun Yanzu: Kashim Shettima Ta Faɗi Kuskuren da Shugaba Buhari Ya Tafka a Mulkinsa Kamar Na Jonathan

Haka nan manyan arewan sun ƙara da cewa wannan bukata da suka gabatar ta baiwa arewa jagorancin ɓangaren majalisar tarayya a gwamnati ya yi daidai da tanadin 14(1), (2) da (3) a kundin dokokin mulki 1999.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jagororin arewan sun aike da wannan buƙata ne a wurin taron kwana ɗaya da ya gudana a Kaduna ranar Jumu'a 12 ga watan Mayu, 2023.

A wurin taron sun maida hankali wajen tattauna batutuwan da suka shafi arewa kamar kalubalen tattalin arziki da kuma gudummuwar yankin a nasarar da Tinubu ya samu a zaɓen 2023.

Manufar taron, wanda ya samu wakilai daga jihohi 19, shi ne tattauna manyan kalubalen da ke tunkarar arewa musamman a bangaren ilimi, Noma da Talauci.

Meyasa arewa ta nemi shugabancin majalisa ta 10?

Sakataren "Northern leader's round-table," Dakta Benjamin Dikki, ya ce duba da gudummuwar da arewa ta angiza wa Tinubu ya ci zaɓe, bai kamata kudu ta sa rai da shugabancin majalisa ba.

Kara karanta wannan

Ta Fasu An Ji: An Fallasa Abinda Tinubu da Gwamna Wike Su Ke Kulla Wa Atiku Abubakar a Kotu

Sun bukaci Sanatocin arewa su nemi kowane kujera a majalisar dattawa ta 10 domin a dama yankin wajen kawo ci gaba.

Atiku da Namadi Sambo Sun Nemi Mambobin PDP Su Cure Wuri 1

A wani labarin kuma Atiku Abubakar da Namadi Sambo sun bayyana alamun cewa PDP zata samu nasara a Kotun zaɓe.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya roki mambobin PDP su dunƙule, da yuwuwar ya karɓi ƙasa.

Haka zalika Namadi Sambo, tsohon mataimakin shugaban ƙasa a mulkin Jonathan, ya koka kan yadda korar mambobi da dakatarwa ke cin kasuwa a PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel