Wayau Za A Yi Wa Tsoho: Zan Je Kotu In Hana Bashin Karshe Da Buhari Yake So, Sanata

Wayau Za A Yi Wa Tsoho: Zan Je Kotu In Hana Bashin Karshe Da Buhari Yake So, Sanata

  • Sanata Muhammad Ali Ndume ba zai yarda da bashin da gwamnatin tarayya ta ke neman karbowa ba
  • Domin ya kalubalanci lamarin, Sanatan kudancin jihar Borno zai yi shari’a da gwamnati a gaban kotu
  • Muhammad Ali Ndume ya na ganin ana neman hanyar da za a saci kudi ne da sunan cin bashi a waje

Abuja - Sanata mai wakitar kudancin jihar Borno a majalisar dattawa, Muhammad Ali Ndume ya sha alwashin yin shari’a da Muhammadu Buhari.

A wata hira da aka yi da shi a tashar talabijin Trust, Sanata Muhammad Ali Ndume ya nuna zai je kotu a dalilin bashin da gwamnatin tarayya ke nema.

Shugaba mai barin-gado ya na so Sanatoci su ba shi dama ya aro bashin Dala miliyan 800 daga bankin Duniya a shirin cire tsarin tallafin man fetur.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari: Cikas 1 da Ya Hana Ni Maganin Barayin Gwamnati a Mulkina

Muhammadu Buhari
Muhammadu Buhari a bakin aiki Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

A zantawar da ya yi da gidan talabijin Trust TV, Muhammad Ali Ndume ya nuna bai dace a karbo wannan bashi ba, kuma ya ce an saba dokar Najeriya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A bisa zargin saba doka da kundin tsarin mulki ne Sanatan na Borno ta Kudu zai yi kara a kotu, a cewarsa zai yi wahala ayi adalci wajen rabon bashin.

Sanatan ya zargi jami’an gwamnati da kawo bashin da nufin yaudarar shugaban kasa, ayi sata.

Maganar da Muhammad Ali Ndume ya yi

"Zan je kotu domin babu adalci, an saba doka da kundin tsarin mulki. Bari in ba ku misali, mu biyu ne dakin nan, sai ka ce za ka karbo N1m domin ka raba mana, wace hanya za ku bi wajen zaben?
Baya ga haka idan za ka raba mana ne sannan mu biya babu matsala, amma kowane ‘dan kasa ne zai biya.

Kara karanta wannan

Shugaban Kasa Yana Landan, Osinbajo Ya Amince a Kafa Sababbin Jami’o’i 36 a Najeriya

Idan ka cinko wasu ‘Yan Najeriya ka raba masu N4000, wani adalci a ka yi a nan? Asali ya ci karo da tsarin mulki domin kundi ya ce ka da a nuna wariya.
Mutanen nan za su yi Ingilishi ne kurum su rikita tsohon nan (Buhari), sai kurum ya amince.
Shi (Muhammadu Buhari) bai fahimci wannan ba, su na so ne suyi amfani da shi ne domin satar kudi kurum, ba za mu bari a cigaba da yin abubuwa irin haka ba."

- Muhammad Ali Ndume

Magana ta na majalisa

An ji labari an bukaci majalisa ta amince a ci bashin $800m. Gwamnati mai barin-mulki ta na ikirarin za ayi amfani da kudin domin a taimakawa talakawa.

Yau mako daya kenan da Muhammadu Buhari ya rubuta wasika zuwa majalisar dattawa da nufin ya karbo bashin kudi da zai iya zama na karshe a mulki.

Kara karanta wannan

Kwanaki 13 Kafin Ya Bar Aso Villa, Buhari Ya Fadi Kokari 3 da Ya Yi Cikin Shekaru 8

Asali: Legit.ng

Online view pixel