Sarki Sanusi II Ya Goyi Bayan Takara, Ya Masa Fatan Alheri a 2027
- Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya taya ɗan majalisar tarayya, Aminu Jaji, murnar nasarar da ya samu a zaɓen fidda gwani na APC da aka maimaita
- Sarkin ya buƙaci Jaji da ya ƙara ƙaimi wajen yi wa al’umma hidima, tare da yi masa addu’ar samun nasara a babban zaɓen 2027
- Sanusi II ya bayyana nasarar ɗan majalisar a matsayin alamar jajircewa, aiki tuƙuru da kuma karɓuwarsa a mazabarsa da sauran wurare.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya taya ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Kaura Namoda/Birnin Magaji a Jihar Zamfara, Aminu Jaji, murnar nasarar da ya samu a zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC da aka sake gudanarwa.
Sarkin ya kuma buƙaci ɗan majalisar da ya ƙara ƙaimi da jajircewa wajen yi wa al’umma hidima, tare da yi masa addu’ar samun cikakkiyar nasara a babban zaɓen 2027.

Kara karanta wannan
Malamin Musulunci ya sha kaye a ƙokarinsa na samun tikitin takarar gwamnan Kano a 2027

Source: Facebook
Leadership ta wallafa cewa wata wasiƙa mai kwanan watan 13 ga Nuwamba, 2026, wadda Khalifa Aliyu Ahmed Abdulfathi ya sanya wa hannu a madadin sarkin, ta bayyana hakan.
Sanusi II ya taya Aminu Jaji murna
A cikin wasiƙar, sarkin ya bayyana nasarar Jaji a zaɓen fidda gwani da aka maimaita a matsayin abin da ke tabbatar da jajircewarsa, aiki tuƙuru, gaskiya da karɓuwarsa a tsakanin al'ummar mazabarsa da ma sauran jama'a.
Wasiƙar ta ce:
“A madadin Mai Martaba Sarkin Kano na 16 kuma Khalifan Darikar Tijjaniyya a Najeriya, Dr Muhammadu Sanusi Lamido Sanusi, muna miƙa maka saƙon taya murna bisa nasarar da ka samu a zaɓen da aka kammala na Kaura Namoda/Birnin Magaji a Jihar Zamfara.”
Sanusi II ya bukaci ya ƙara ƙaimi
Sanusi II ya bayyana cewa Majalisar Shura ta Darikar Tijjaniyya ta san irin jajircewar Jaji wajen hidimar al’umma, inda ta gode wa Allah bisa nasarar da ya samu.
Ya buƙaci ɗan majalisar da ya ƙara ƙoƙari da sadaukarwa wajen gudanar da ayyukansa, tare da yi masa addu’ar samun nasara a zaɓen 2027.

Source: Original
Haka kuma, The Nation ta wallafa cewa sarkin ya yi addu’ar samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a Jihar Zamfara da sauran sassan Najeriya.
Rahotanni sun nuna cewa mai martaba sarkin ya kuma yi fatan za a gudanar da babban zaɓen 2027 cikin nasara da lumana.
Sanusi II ya je Zamfara
A wani labarin, kun ji cewa Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya karɓi baƙuncin Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, wanda ya jagoranci buɗe masallacin Juma'a.
Babban limamin Abuja, Farfesa Ibrahim Maqari, shi ma ya halarci taron, inda ya jagoranci sallar Juma’a a masallacin mai dimbin tarihi.
Bayan taron, wasu masu amfani da Facebook sun yaba da aikin sabunta masallacin, yayin da wasu suka yi amfani da damar wajen sukar gwamnatin Zamfara kan matsalar tsaro da ke addabar jihar.
Asali: Legit.ng
