Majalisa ta 10: Gwamnonin APC Za Su Sanya Labule Domin Neman Mafita

Majalisa ta 10: Gwamnonin APC Za Su Sanya Labule Domin Neman Mafita

  • Gwamnonin jam'iyyar APC za su gudanar da taro domin samar da mafita kan shugabancin majalisa ta 10
  • Ana sa ran taron na gwamnonin zai samar da mafita mai kyau kan rikicin shugabancin majalisa ta 10
  • Shugabancin majalisa ta 10 ya jefa jam'iyyar APC a cikin ruɗani da rarrabuwar kai, inda da dama daga cikin ƴaƴan jam'iyyar suka yi fatali da tsarin jam'iyyar

FCT Abuja - Gwamnonin jam'iyyar All Progressives Congress (APC), za su yi taro yau Litinin, 15 ga watan Mayun 2023, kan rikicin shugaban majalisa ta 10.

Jaridar Leadership ta kawo rahoto cewa, taron na zuwa ne bayan wasu gwamnoni, sun cigaba da yin kamun kafa domin ganin an bar tsarin da jam'iyyar ta kawo kan shugabancin majalisar.

Gwamnonin APC za su sanya labule kan shugabancin majalisa ta 10
Wasu daga cikin gwamnonin APC tare da shugaba Buhari Hoto: Premiumtimes.com
Asali: UGC

Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu wanda shine shugaban ƙungiyar gwamnonin Kudancin Najeriga, ya soki tsarin na APC, inda ya bayyana shi a matsayin wanda ba zai kai labari ba, mai cike da kura-kurai da rashin adalci.

Kara karanta wannan

Gwamnan Jihar Taraba Ya Bayyana Gaskiya Dangane Da Batun Fitar Da N2bn a Asusun Jihar Domin Siyo Motocin Kece Raini

Jaridar Punch tace wani majiya dangane da taron, ya bayyana cewa taron, zai samar da mafitar da ta dace dangane da rikicin shugabancin wanda ya ƙi ci ya ƙi cinyewa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyar ya bayyana cewa:

"Mu na da cikakken ƙwarin guiwa kan cewa idan gwamnonin APC sun yi taro yau, za su bayar da shawarwari masu kyau da mafita kan wannan rikicin da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa."

Jam'iyyar APC, ta hannun kwamitin gudanarwar ta na ƙasa (NWC), ta kai kujerun shugabancin majalisar dattawa yankin Kudu maso Kudu (Sanata Godswill Akpabio), mataimakin shugaban majalisar dattawa yankin Arewa maso Yamma (Barau Jibrin)

Jam'iyyar ta kuma kai kujerun kakakin majalisar wakilai yankin Arewa maso Yamma (Hon. Abbas Tajudeen) mataimakin kakakin majalisar wakilai yankin Kudu maso Yamma (Benjamin Kalu).

Sai dai shugaban jam'iyyar na ƙasa, Abdullahi Adamu, a satin da ga gabata ya yi nuni da cewa jam'iyyar za ta sake yin duba kan wannan tsarin na ta, da ta fitar kan shugabancin majalisa ta 10.

Kara karanta wannan

Wasu Wurare 4 da Bola Tinubu Zai Iya Shan Wahala Bayan Ya Gaji Muhammadu Buhari

Sanatan APC Ya Sha Gaban Yari a Takarar Majalisa, Ya Fadi Sanatocin da ke Tare da Shi

A wani rahoton na daban kuma, kun ji cewa Sanata Godswill Akpabio, ya bayyana adadin yawan Sanatocin da ke tare da shi a ƙoƙarinsa na zama shugaban majalisar dattawa.

Akpabio wanda tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom ne, ya bayyana cewa sanatocin da ke tare da shi sun kusa 100.

Asali: Legit.ng

Online view pixel