Mafi karancin albashi
Shugaban ASUU, Emmanuel Osodeke ya aika takarda zuwa ga ‘Yan ASUU cewa su dakatar da zuwa aiki duk da ba a biya su albashin wata 8 ba na yajin-aikin kwanaki.
Cibiyar Nazarin Ayyukan Majalisa da Dimokuradiyya ta Najeriya (NILDS) ta bukaci a kara kudaden da ake ware wa majalisa domin ayyukan sa ido ga bangaren zartarwa.
Kungiyar Kwadago a Najeriya, NLC ta tura sakon gargadi ga gwamnati kan kame shugabanta, Joe Ajaero, ta ce za ta durkusar da Najeriya da yajin aiki.
Ganin ya zama Sanata, tsohon gwamna a Gombe, Ibrahim Hassan Dankwambo ya bukaci gwamnatin jiharsa ta dakatar da biyansa kudin fanshon da aka saba ba shi duk wata.
NLC ta yi bayanin abin da ya sa ba za ta shiga duk taro da Simon Lalong zai halarta ba, ta ce taron da za ayi da gwamnatin tarayya, Ministan ba zai shiga ciki ba.
Bayan tantacewar IPPIS, Gwamnatin Najeriya za ta daina biyan albashin wasu ma’aikata. Duk wanda ba a iya tantacewa ba, za a cire sunansa daga masu cin albashi.
Kungiyar Kwadago ta Najeriya, NLC ta bayyana cewa nan ba da jimawa ba za su fara tattaunawa da gwamnati kan mafi karancin albashi dubu 100 ko 200.
Kungiyar kwadago ta yi karin-haske a kan yajin-aikin da aka fasa shiga a makon nan, amma nan da kwanaki 30 za su waiwayi duk alkawuran da gwamnati ta dauka.
Shugabannin kungiyoyin NLC da TUC sun hakura da zuwa yajin-aiki. Kafin ‘yan kwadago su lashe amansu, sai da aka cin ma wasu yarjejeniya da gwamnatin Najeriya.
Mafi karancin albashi
Samu kari