Shugaba Tinubu Ya Fara Shirin Kara Albashin Ma’aikata, An sa Ranar Kafa Kwamiti

Shugaba Tinubu Ya Fara Shirin Kara Albashin Ma’aikata, An sa Ranar Kafa Kwamiti

  • Gwamnatin tarayya za ta rantsar da kwamitin da zai duba lamarin karin albashin da za ayi wa ma’aikata
  • Sanata George Akume ya sanar da wannan a wata wasika ta musamman da ya turawa shugabannin NLC
  • A karshen zaman wannan kwamiti, za a kawo shawarar karin kudi mafi karancin albashi da za a biya a kasa

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Najeriya ya amince da kafa wani kwamiti da zai yi aiki a kan tsarin albashi.

Wannan kwamiti zai yi nazarin mafi karacin albashi da ake biyan ma’aikata kamar yadda Legit ta fahimta daga bayanai.

Karin albashi
Shugaban kasa ya yarda a kafa kwamitin karin albashi Hoto: @Dolusegun16, @imranmuhdz
Asali: Twitter

Kwamitin karin albashi a Najeriya

Mun ci karo da wannan takarda da ta fito daga Sanata George Akume OFR wanda shi ne Sakataren gwamnatin tarayya.

Kara karanta wannan

Matashi da ya mallaki naira miliyan 30 ya samu karayar arziki, ya koma rokon N2k

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata George Akume ya aika wasikar zuwa ga shugabannin kungiyar kwadago na kasa masu neman ayi karin albashi.

Kungiyoyin NLC ta TUC sun dage cewa dole ayi karin albashi a sakamakon cire tallafin fetur da gwamnati ta yi a 2023.

Albashin ma'aikata zai karu a 2024

Sakataren gwamnatin tarayya ya shaida cewa mai girma Bola Tinubu ya nanatawa ma’aikata zai kara masu albashi.

Rantsar da wannan kwamiti zai tabbatar da an yi hobbasa wajen ganin ma’aikaci ya samu abin da zai iya rike shi a wata.

Bayanin taro a kan karin albashi

Wasikar da aka aikawa Ambali Akeem Olatunji tace za a rantsar da kwamitin ne a ranar Talata, 30 ga Junairun 2023.

Za a shirya wannan taro da karfe 11:30 na safiya a wani babban zaure a fadar shugaban Najeriya a babban birnin Abuja.

Kara karanta wannan

An kawo jami’ai 140 su auna Ministoci, su bada shawarar wadanda za a bari a ofis

Akwai motoci da za su dauki masu halartar taron, The Cable ta fitar da sashen labarin.

Kwamitin Bukar Goni Aji zai yi aikin karin albashi

Hadimin shugaban kasa, Olusegun Dada, a bayanin da ya yi a X, yace Alhaji Bukar Goni Aji zai jagoranci wannan kwamiti.

Akwai mutane 37 a karkashin Bukar Goni Aji wanda ya taba zama shugaban ma'aikatan gwamnatin tarayya a kasa.

Halin da albashin ma'aikata yake ciki a yau

A shekarar 2019 ne Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a dokar da ta ba ma’aikaci damar karbar akalla N30, 000 a wata.

Zuwa yanzu rayuwa ta kara tsada sosai Najeriya, don haka ake neman karin albashi.

Bayan farashin fetur da ya tashi a shekarar bara, abinci sun yi tsadar da ake hasashen ba za suyi araha a nan kusa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng