Peter Obi
Farfesa Farouq Kperogi ya yi bayanin dalilin da ya sanya Peter Obi da Atiku Abubakar suka kasa yin nasara a kan Shugaba Bola Ahmed Tinubu a kotu.
Gwamna Alex Otti na jihar Abia tun bayan hawanshi mulki bai taba zama a sabo ko tsohon gidan gwamnati ba, daga kauyensu ya ke gudanar da mulkin jihar.
Cibiyar CLE ta dakatar da Jami'ar Baze da ke Abuja saboda wasu dalilai da dama da su ka hada kammala karatun digiri a cikin shekaru uku kacal wanda ya saba wa doka.
Dan takarar jam’iyyar LP, Peter Obi ya shiga sahun yan siyasa wajen taya Atiku Abubakar murna yayin da ya cika shekaru 77 a duniya. Ya kira shi da babban yayansa.
Alkalin Alkalin Najeriya (CJN) Olukayode Ariwoola, ya yi shagube ga Atiku da Peter Obi yayin da ya bayyana inda za a iya daukaka kara bayan hukuncin kotun koli.
An buƙaci ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar da ya ceto jam'iyyar a zaɓen 2027, inda aka gaya masa hanya mafi sauƙi da zai yi hakan.
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, ya soki kalaman da Shugaba Tinubu ya yi na cewa ya gaji tarin basussuka a ƙasa.
Jam'iyyar LP a Najeriya ta yi martani kan jita-jitar cewa sun hada kai da sauran jam'iyyun adawa don kwace mulki a hannun APC mai mulki, sun fadi gaskiya.
Atiku Abubakar ya fara kiran ‘yan adawa su yi wa jam’iyyar APC taron dangi a zaben 2027. NNPP ta ce idan Atiku yana so ayi taron dangi, akwai sharadi guda.
Peter Obi
Samu kari