'Za a Hada Kai': Atiku Ya Bude Baki a Karon Farko Bayan Zama da Peter Obi

'Za a Hada Kai': Atiku Ya Bude Baki a Karon Farko Bayan Zama da Peter Obi

  • Mataimakin Shugaban kasar Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar na tattaunawa da tsohon dan takarar shugaban kasa karkashin Labor Party domin dunkulewa wuri guda
  • Wannan wani mataki ne na samar da hadakar da su ke fatan zai tunbuke jam’iyyar APC karkashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu daga mulki
  • Alhaji Atiku Abubakar da ya tsayawa PDP takarar shugabancin kasar nan a zaben 2023 ya bayyana cewa zai marawa duk wanda ya cancanta baya a 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja- Tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben 2023 karkashin jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa tattaunawarsa da takwaransa na Labor Party na duba yiwuwar hadewa wuri guda kafin zabe na gaba.

Kara karanta wannan

Siyasar 2027: Ka yi hankali da mutanen Arewa, Ibo sun fara gargadin Peter Obi

Wannan na daga matakin jam’iyyun adawa na duba yiwuwar kawo karshen mulkin shugaba Bola Ahmed Tinubu a filin zabe.

Atiku Abubakar, Peter Obi
2027: Ana tattaunawa tsakanin Atiku Abubakar da Peter Obi Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

A rahoton da BBC Hausa ta wallafa, an ji cewa tattaunawar shugabannin biyu ta yi nisa, inda su ka bayyana fatansu na ceto kasar nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku/Obi: Wa za a tsaida takara?

Jam’iyyar LP ta bayyana cewa jagoranta Peter Obi na tattaunawa da Alhaji Atiku Abubakar da sauran ‘yan siyasa a Arewa domin ceto Najeriya, kamar yadda The Guardian ta wallafa.

Tsohon mataimakin shugaban kasar nan, Atiku Abubakar kuma daya daga masu zawarcin kujerar shugaban kasa ya bayyana cewa ya na tare da duk wanda ya cancanci tsayawa takara a 2027.

Duk da Atiku bai fito kai tsaye ya kama sunan Peter Obi ba, amma ya bayyana cewa zai iya marawa wanda ya fito daga kudu maso gabashin kasar nan baya domin kwato Najeriya daga hannun Tinubu.

Kara karanta wannan

Tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa ya sauya sheƙa zuwa APC

Ana gangamin kwace mulki a 2027

A baya mun kawo mu ku labarin cewa tsohon dan takarar shugaban kasa, Pat Utomi ya bayyana cewa babu jam’iyyar da za ta iya ceto Najeriya daga kangin da aka jefa ta.

Saboda haka ne ma ya kara da cewa ana gangamin hada kawunan masu kishin kasa, domin samar da adawa mai karfi da za ta kwace mulki daga hannun APC a kakar zaben 2027.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.