Daga Karshe An Fadi Dalilin da Zai Sanya Peter Obi Ya Koma PDP

Daga Karshe An Fadi Dalilin da Zai Sanya Peter Obi Ya Koma PDP

  • Tsohon shugaban ƙungiyar yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam'iyyar LP ya yi magana kan yiwuwar Peter Obi ya koma jam'iyyar PDP
  • Akin Osuntokun ya bayyana cewa Peter Obi zai koma PDP ne kawai idan za a ba shi tikitin yin takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027
  • Ya yi nuni da cewa koma baya ne a wajen tsohon ɗan takarar shugaban ƙasar idan ya zama mataimakin ɗan takarar da PDP za ta tsayar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Tsohon shugaban ƙungiyar yaƙi neman zaɓen Peter Obi a matsayin shugaban ƙasa a 2023, Akin Osuntokun, ya yi magana kan yiwuwar ɗan takarar ya koma jam'iyyar PDP.

Akin Osuntokun ya bayyana cewa Peter Obi zai koma jam'iyyar PDP ne kawai idan za a ba shi tikitin yin takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

"Zamu karɓe wasu jihohi," Ganduje ya bayyana abubuwa 2 da APC ta shirya a 2027

Yiwuwar komawar Peter Obi zuwa PDP
Peter Obi ya yi takarar shugaban kasa a zaben 2023 Hoto: Mr Peter Obi
Asali: Facebook

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa idan a shekarar 2027, jam’iyyar ta zaɓi Peter Obi a matsayin ɗan takararta, zai goya masa baya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me zai sa Peter Obi ya koma PDP?

Da yake mayar da martani kan hakan a wata hira da tashar Arise tv, Akin ya ce duba da goyon bayan da Peter Obi ya samu a zaɓen 2023, zai koma PDP ne kawai idan za a ba shi tikitin yin takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar.

"Komawar Peter Obi zuwa PDP zai dogara ne daga tabbacin da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar za su ba shi."
"Maganar gaskiya ita ce ba abu ba ne mai yiwuwa wanda ya yi takarar shugaban ƙasa yanzu kuma ya dawo ya amince ya zama mataimakin duk wanda aka ba takara."

Kara karanta wannan

Ganduje: Shirin tsige shugaban APC na ƙasa da maye gurbinsa ya gamu da cikas

"Hanya ɗaya kawai da Peter Obi zai duba yiwuwar komawa PDP ita ce idan za a ba shi tikitin takarar shugaban ƙasa. Idan ba haka ba, ba zai yi wannan kasadar ba."
"Saboda idan ya zama abokin takarar wani a PDP, zai rasa ɗumbin magoya bayansa. Za a zarge shi da zama mai siyasa saboda kuɗi."

- Akin Osuntokun

Batun haɗewar Peter Obi da Atiku

A wani labarin kuma, kun ji cewa hankalin jam’iyyar APC ya fara karkata kan tattaunawar yin haɗaka tsakanin Atiku Abubakar na PDP Peter Obi na LP.

Jam'iyyar ta hannun sakatarenta na ƙasa ta ce yan siyasar biyu na ƙoƙarin haɗewa ne kawai saboda tsabar takaicin da ke tattare a zuciyoyinsu game da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel