Kotu Ta Raba Gardama Kan Sahihancin Zaben Gwamnan APC, Ta Jero Hujjoji

Kotu Ta Raba Gardama Kan Sahihancin Zaben Gwamnan APC, Ta Jero Hujjoji

  • Yayin da ake shari'a kan zaben jihar Imo, kotu ta yanke hukunci kan tabbatar zaben da aka gudanar
  • Kotun sauraran kararrakin zaben jihar ta tabbatar da nasarar Gwamna Hope Uzodinma na jami'yyar APC
  • Kotun ta yi fatali da korafe-korafen ɗan takarar jam'iyyar LP, Athan Achonu saboda rashin hujjoji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Imo - Kotun sauraran kararrakin zabe a jihar Imo ta yi hukunci kan zaben gwamnan jihar.

Kotun ta tabbatar da nasarar Gwamna Hope Uzodinma na jami'yyar APC a matsayin zaɓaɓɓen gwamnan jihar.

Kotu ta yi hukunci kan shari'ar zaben gwamnan APC
Kotu ta tabbatar da nasarar Gwamna Hope Uzodinma na jami'yyar APC a Imo. Hoto: Hope Uzodinma.
Asali: Facebook

Imo: Matakin kotu kan zabe APC

Har ila yau, kotu ta yi fatali da korafin ɗan takarar jami'iyyar LP, Athan Achonu da ke kalubalantar zaben, cewar The Nation.

Kara karanta wannan

Jami'an DSS sun mamaye fadar Sarkin Kano? Gaskiyar abin da ya faru ta bayyana

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alkalan kotun guda uku karkashin jagorancin Mai Shari'a, Oluyemi Akintan-Osadebay su suka yanke hukunci kan zaben.

Alkalan sun tabbatar da cewa Uzodinma shi ya lashe zaben kuma bai saba duk wata doka ta hukumar zabe ba, Vanguard ta tattaro.

Kotun ta kuma ce jam'iyyar LP ta dan takararta sun gaza kawo gamsassun hujjoji kan rashin bin ka'idar zabe da suke zargin APC da kuma kara kuri'u a zaben.

INEC ta ba gwamna Uzodinma nasara

Wannan na zuwa ne bayan hukumar zaben ta tabbatar da Hope Uzodinma na APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar.

Uzodinma ya samu kuri'u 540,308 yayin da mai bi masa dan takarar PDP, Samuel Anyanwu ya samu kuri'u 71,503 sai kuma Achonu ya zo na uku da kuri'u 64,081.

An gudanar da zaben ne a watan Nuwambar shekarar 2023 da sauran jihohin Kogi da Bayelsa.

Kara karanta wannan

Majalisar Kano ta rusa duka Sarakunan da Gwamnatin Ganduje ta kirkiro a 2019

Gwamna Uzodinma ya nada kansa kwamishina

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Hope Uzodimma ya nada kansa a matsayin kwamishinan filaye na jihar Imo.

Wannan sanarwar ta bazata ta fito daga bakin gwamnan a ranar Talata, yayin rantsar da sabbin kwamishinoni 24 na jihar a gidan gwamnati da ke Owerri.

A cewar Uzodinma, nada kansa mukamin wani mataki ne na hana sake afkuwar al’amuran da suka faru a baya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel