Yanzu ta tabbata, Kwankwaso Zai Fice daga NNPP, An Faɗi Jam'iyyar da Zai Koma
- Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kammala shirye-shiryen komawa jam'iyyar ADC domin fuskantar zaben shekarar 2027
- Kakakin kungiyar Kwankwasiyya ya bayyana cewa jagoran nasu fice daga jam'iyyar NNPP a hukumance a gidansa na Miller Road
- An ba dukkan mambobin Kwankwasiyya umarnin gaggawa na su garzaya mazabunsu domin yin rajista da jam'iyyar ADC
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Jagoran darikar Kwankwasiyya na ƙasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ba mambobinsa umarnin sauya sheka zuwa jam'iyyar ADC.
Wannan sanarwa tana zuwa ne a matsayin wani babban matakin siyasa da tsohon gwamnan na jihar Kano ya ɗauka domin fuskantar zaɓen shekarar 2027.

Source: Facebook
Kwankwaso zai sauya sheka zuwa ADC
Wannan na kunshe ne a cikin sanarwar da mai magana da yawun Kwankwaso, Hon. Saifullahi Hassan ya wallafa a shafinsa na X.
A cikin sanarwar, an ruwaito kakakin ƙungiyar Kwankwasiyya, Dr. Habibu Sale Mohammed, ya ce Kwankwaso ya kammala dukkan tsare-tsare na shiga jam'iyyar hadakar 'yan adawa.
Ƙungiyar Kwankwasiyya ta sanar da mambobinta da sauran jama'a cewa jagoransu zai yi rajista da sabuwar jam'iyyar tasa a hukumance ranar Litinin mai zuwa.
Za a gudanar da wannan taro ne da misalin ƙarfe 12:00 na rana a gidan Kwankwasiyya dake Miller Road a cikin birnin Kano.
An tsara cewa Sanata Kwankwaso zai karɓi katin jam'iyyar ADC a gaban dubun-dubatar magoya bayansa waɗanda ake sa ran za su cika gidan nasa.
Umarni ga 'ya'yan Kwankwasiyya a Najeriya
Biyo bayan wannan mataki, an umarci dukkan 'yan ƙungiyar Kwankwasiyya dake fadin Najeriya da su garzaya su yi rajista da jam'iyyar ADC a mazaɓunsu, in ji rahoton Daily Trust.
Dr. Habibu ya jaddada cewa ya zama dole mambobi su shiga harkokin jam'iyyar a matakin gundumomi da ƙananan hukumomi domin tabbatar da nasarar sabuwar tafiyar.
An buƙaci magoya bayan da su jajirce wajen ganin jam'iyyar ta samu gindin zama a kowane lungu da sako na ƙasar nan gabanin 2027.
Dalilin sauya sheƙar Kwankwaso zuwa ADC
Kakakin Kwankwasiyya ya bayyana cewa wannan mataki an ɗauke shi ne domin kare muradun dimoƙuradiyya da kuma samar da kyakkyawan shugabanci a faɗin Najeriya.
Sanarwar ta ƙara da cewa Kwankwasiyya tana son gina ƙasa da za ta jibinci lamuran kowa da kowa inda za a girmama ra'ayin talakawa a duk lokacin zaɓe.
Wannan sauya sheƙa na Kwankwaso na nuna cewa jam'iyyar NNPP ta rasa babban bango majinginarta, kuma ba lallai ne ta yi tasiri a zaben 2027 ba.
Karanta sanarwar a nan kasa:
Abin da wasu ke cewa kan matakin Kwankwaso
Legit Hausa ta zanta da Abba Hassan Gezawa daga jihar Kano, wanda ya ce:
"Mu kafarmu kafar Kwankwaso, duk inda ya shiga to muna a bayansa. Ai wallahi ban ji ina son sa ba sai da Abba ya koma APC, nan na kara yarda cewa Kwankwaso abin koyi ne.
"Ka duba fa, haka Ganduje ya yi masa, bayan ya taimake shi ya hau gwamna, yanzu ma Abba ya juya masa baya, bayan duk wahalar da ya yi masa har ya zama gwamna."
Abba Gezawa ya ce suna jiran 2027 ta zo don nunawa Abba cewa Kano ta Kwankwaso ne, furar da ya dama ce za a sha.
Amma kuma, Usman A.T.O, Kabuga, jihar Kano, ya nuna cewa abin da Abba ya yi ba butulci ba ne, ya duba mafitarsa ne kawai, kamar yadda shi ma yanzu Kwankwaso zai shiga ADC don mafitarsa.
"Ai yanzu Malam Sani, kowa ya kara gane cewa siyasa kasuwar bukata ce. Ai idan aka ce Abba ya yi butulci, to za mu iya cewa jagora ma ya yi kenan, tun da ya bar NNPP, inda ake ganin nan ne gidansa.
"Mu har gobe muna ganin martaba da kimar Kwankwaso, kuma har gobe zan iya yin fada da duk wanda zai taba mutuncin jagora, amma fa, ba zan zagi Abba don ya koma APC ba, sannan in zo ina kare Kankwaso don ya shiga ADC ba, kowa ya duba mafitarsa ne kawai."
- Usman A.T.O.
Kwankwaso ya yi murabus daga NNPP
A wani labari, mun ruwaito cewa, tsohon gwamnan Knao, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya tabbatar da yin murabus daga daga jam’iyyar NNPP mai adawa.
Kwankwaso ya bayyana wannan mataki da ya dauka a matsayin mai wahala, yana mai cewa sauyin siyasa a kasa ya tilasta masa haka.
Rahotanni sun nuna cewa Kwankwaso na shirin komawa ADC inda ake sa ran zai bayyana matsayarsa a Kano nan ba da jimawa ba.
Asali: Legit.ng



