Abu Ya Girma: Kwankwasiyya Ta Nuna Yatsa ga Gwamna Abba kan Zargin Muzgunawa 'Yan Adawa
- Kungiyar Kwankwasiyya ta fito ta yi zarge-zarge kan gwamnatin jihar Kano wadda Gwamna Abba kabir Yusuf ke jagoranta
- Kwankwasiyya ta nuna damuwa kan abin da ta kira karuwar cin zarafin 'yan adawa da gwamnatin Kano ke yi tun bayan hadewa da APC
- Ta nuna cewa abin da gwamnatin ke yi na toshe bakin 'yan adawa na jawo abin kunya a idon duniya ga jihar Kano
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Kungiyar Kwankwasiyya ta yi zarge-zarge kan gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Kwankwasiyya ta yi Allah-wadai da abin da ta bayyana a matsayin karuwar dabarun tsoratarwa ta siyasa, cin zarafi, da tsare ’yan ƙasa ba bisa ƙa’ida ba a Kano, inda ta zargi mahukunta da danne ’yancin faɗar albarkacin baki.

Source: Facebook
Jaridar Tribune ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da daya daga cikin masu magana da yawun Kwankwasiyya, Mansur Umar Kurugu, ya fitar a ranar Laraba, 25 ga watan Fabrairun 2026.
Kwankwasiyya ta damu kan salon Gwamna Abba
Kungiyar Kwankwasiyya ta bayyana wannan lamari a matsayin wani mummunan mataki na danne muryoyin adawa.
“Tun bayan ficewar gwamna zuwa tsarin siyasar APC/Gandujiyya, jihar Kano ta shaida wata damuwa ta karuwar amfani da hukumomin tsaro domin toshe bakin masu suka."
"Wannan ba abin amincewa ba ne, rashin haƙuri ne na siyasa, kuma yana nuna rauni maimakon shugabanci.”
- Mansur Kurugu
Amnesty ta yi zargi kan gwamnatin Kano
Ya yi nuni da rahoton kungiyar Amnesty, wanda aka ce ya tattara bayanan mutanen da aka kama ko kuma aka “gayyata” domin yi musu tambayoyi kan kalaman da suka yi a intanet.
Daga cikin waɗanda rahoton ya ce abin ya shafa har da Abba Ibrahim Hussain, Aminu Warkal, Samir Hanga, Abdulmajid Danbilki Kwamanda, da Saifullahi Abubakar, waɗanda ake zarginsu da suka, sharhi, ko kuma yin ba’a ga jami’an gwamnati.
Kwankwasiyya ta kausasa harshe kan gwamnatin Kano
“Babu wata al’ummar dimokuraɗiyya da take mayar da adawa a matsayin laifi, kuma babu wani shugaba da ya fi ƙarfin suka."

Kara karanta wannan
Kwankwaso ya yi magana bayan ganawa da gwamnan PDP, ya tabo abin da suka tattauna
"Mayar da hukumomin tsaro makamin yaƙi da ’yan ƙasa yana raunata dimokuraɗiyya kuma yana gurgunta amincewar jama’a ga gwamnati.”
- Mansur Kurugu
Sanarwar ta nuna takaicinta kan abin da ta bayyana a matsayin kaucewa daga tarihin siyasar Kano, inda ta ambaci tarihin fitattun shugabanni irin su Aminu Kano, Abubakar Rimi, Sabo Bakin Zuwo, da Rabiu Musa Kwankwaso, jaridar The Punch ta kawo labarin.
“Abin ban takaici ne yadda gwamnatin Kano, jihar da ke da dogon tarihin siyasa wanda ya samar da mutane irin su Malam Aminu Kano da sauran su, za ta yi watsi da siyasar ra’ayi da tseren kawo ci gaba ta koma kan tsoratarwar siyasa da kuma kunyata kanta."
- Mansur Kurugu

Source: Facebook
Kwankwasiyya ta ce gwamnati na kunyata Kano
Kungiyar ta nuna cewa wannan danniya da ake zargi tana lalata martabar Kano a idon duniya, tana mai cewa ana ambaton jihar a rahotannin duniya saboda munanan dalilai maimakon nasarorin ci gaba.
“Kano tana bayyana a rahotannin ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa ba don kyakkyawan ci gaba ba, sai dai don labaran danne ’yan adawa. Wannan abin takaici ne."
Ƙungiyar ta yi watsi da abin da ta kira siyasar ban tsoro, sannan ta yi gargaɗi game da yin amfani da ikon gwamnati ta hanyar da ba ta dace ba wajen tsoratar da abokan hamayya da talakawa.
“Tsoratarwa ba za ta dakatar da mu ba. Cin zarafi ba zai sa mu yi shiru ba. Kamu ba zai raunata kudurinmu ba."
- Mansur Kurugu
Majalisa ta mika bukata ga Gwamna Abba
A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar dokokin jihar Kano ta mika bukatarta ga Gwamna Abba Kabir Yusuf kan zargin da Amurka ke yi wa Kwankwaso.
Majalisar ta bukaci Abba Kabir da ya dauki matakin mayar da martani kan wasu zarge-zarge da Amurka ke yi wa tsohon gwamnan jihar.
Bukatar na zuwa ne dai bayan wasu 'yan majalisar Amurka sun bukaci a sanyawa Kwankwaso takunkumi kan zargin muzgunawa Kiristoci.
Asali: Legit.ng

