Halin da Tsohon Shugaban APC, Oshiomhole Ya Shiga bayan Tsige Shi a Mulkin Buhari
- Tsohon shugaban APC na kasa, Adams Oshiomhole ya bayyana irin halin kadaicim da ya tsinci kansa a ciki bayan an tsige shi a 2020
- Sanata Oshiomhole mai wakiltar Edo ta Arewa ya ce mutane sun gudu sun barsa lokacin da ya rasa matsayinsa a jam'iyyar APC
- Ya ce gwamnan Ribas a wancan lokacin, Nyesom Wike ne kadai ya jawo shi a jiki, ya gayyace shi zuwa Fatakwal kuma ya ba shi lambar yabo
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Edo, Nigeria - Tsohon gwamnan jihar Edo, Sanata Adams Oshimhole ya tuna yadda rayuwa ta sauya masa bayan tunbuke shi daga kujerar shugabancin jam'iyyar APC ta kasa.
Oshiomhole, wanda ke wakiltar Edo ta Arewa a Majalisar dattawan Najeriya ta 10, ya ce mutanen da ke tare da shi sun watse sun bar shi bayan ya rasa mukaminsa a APC.

Source: Facebook
Jaridar Tribune Nigeria ta tattaro cewa Oshiomhole ya bayyana hakan ne yayin bikin mika kayan aikin gine-gine guda 54 ga ƙananan hukumomi 18 na Jihar Edo.
Abin da ya faru bayan cire Oshiomhole a APC
Da yake bayyana abubuwan da suka biyo bayan cire shi daga mukamin Shugaban APC na kasa, Sanata Adams Oshiomhole ya nuna cewa lokacin ya kasance na kaɗaici da wariya a siyasance.
A cewarsa, bayan an sauke shi daga mukamin, ’yan jam’iyyarsa da dama sun nisance shi saboda tsoron kada a ɗauki hulɗa da shi a matsayin abin da ya saɓa wa jam’iyyar APC.
“Bayan an cire ni daga shugabancin APC na ƙasa, na zama ni kaɗai. Jam’iyyata ta yi watsi da ni, mutane suna tsoron zuwa su gaishe ni saboda kada a ce suna aikata abin da ya saɓa wa jam’iyya,” in ji shi.
Oshiomhole ya tuna da Nyesom Wike
Sai dai tsohon gwamnan na Edo ya bayyana cewa Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya nemi shi a wancan lokacin, cewar rahoton Punch.
Ya ce Wike ya kira shi tare da gayyatarsa zuwa birnin Fatakwal domin ƙaddamar da wata gadar sama, har ma ya karrama shi da lambar yabo mafi girma ta Jihar Rivers.
“Na samu kira daga wani ɗan Najeriya wanda ya bayyana kansa da mai tausaya wa wadanda ke halin kadaici.
"Ya gayyace ni zuwa Fatakwal domin ƙaddamar da gadar sama. Ba ma haka kaɗai ba, ya ba ni lambar yabo mafi girma ta Jihar Rivers,” in ji Oshiomhole."

Source: Twitter
Ya ƙara da cewa duk da cewa Wike ya taɓa gaya masa cewa ya yi murnar matsalolin siyasar da ya shiga, amma hakan bai hana shi ƙarfafa masa gwiwa a lokacin da yake cikin mawuyacin hali ba.
Oshiomhole ya cika baki kan arahar abinci
A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Adams Oshiomhole ya bayyana cewa arahar abinci ta fara yi wa 'yan Najeriya yawa saboda matakan da Shugaba Tinubu ya dauka.
Oshiomhole, tsohon gwamnan jihar Edo ya yi ikirarin cewa farashin abinci ya sauka ne sakamakon tsare-tsaren da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta aiwatar bayan hawa mulki.
Haka zalika, Sanatan ya nuna goyon bayansa ga sababbin dokokin haraji na shugaban kasa, inda ya bayyana su a matsayin tsari na cigaba.
Asali: Legit.ng


