Shirin Tsige Gwamna Fubara a Majalisa Ya Gamu da Tangarda, Yan Majalisa 2 Sun Canza Tunani
- Majalisar dokokin jihar Ribas ta fara samun sabani da mambobinta kan shirin tsige Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa
- 'Yan Majalisa biyu daga cikin wadanda suka yarda a tsige Fubara tun farko, sun sauya tunani kuma su nemi a dakatar da shirin
- Sun bukaci 'yan Majalisa su sanya wa zuciyoyinsu ruwan sanyi, su koma teburin tattaunawa domin samun masalaha a siyasar Ribas
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Rivers, Nigeria - Majalisar dokokin jihar Ribas ta fara rabuwwa gida biyu kan yunkurin tsige Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa, Farfesa Ngozi Odu.
Biyu daga cikin mambobin majalisar sun roki abokan aikinsu da su maida wukarsu kube, su hakura da shirin tsige Gwamna Fubara daga mukaminsa.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa 'yan Majalisar sun bayyana wannan matsaya ne a wani taron manema labarai da suka kira a Fatakwal, babban birnin jihar Ribas.
Yan Majalisa 2 sun canza tunani a Ribas
Shugaban masu rinjaye na Majalisar dokokin Ribas, Hon. Sylvanus Nwankwo, da mamba mai wakiltar mazabar Degema, Peter Abbey ne suka nemi dakatar da shirin sauke Fubara.
Da yake jawabi, Nwankwo ya bukaci takwarorinsa da su yi adalci da hakuri, inda ya kafa hujjoji da kiraye-kirayen shugabannin al'umma da wasu masu ruwa da tsaki ke yi na a kyale Fubara.
“Mun fitar da sanarwar tsige gwamna, amma sakamakon sa bakin da aka yi, muna roƙon a yi sassauci, sannan a koma teburin tattaunawa domin warware sabani,” in ji shi.
A nasa bangaren, Hon Peter ya yi kira da a samu zaman lafiya, yana roƙon ‘yan majalisar da su dakatar da yunkurinsu na tsige gwamnan.
Yadda za a samu masalaha a Ribas
'Dan Majalisar ya ce duk da ya gamsu Gwamna Fubara da mataimakiyarsa sun karya tanadin kundin tsarin mulki, amma ya fi fifita sulhu a matsayin mafitar kowace matsala.
Hon. Abye ya bukaci a zauna lafiya a jihar Ribas, sannan ya sake kira ga abokan aikinsa da su dakatar da shirin cire gwamnan nan take.
"Idan mu ka rungumi sassauci da yafiya za mu ƙarfafa damar samun zaman lafiya a harkokin mulki tare da ba wadanda ake shirin tsigewa dama su gyara kura-kuransu,” in ji Abbey.

Source: Twitter
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya tuna cewa ‘yan majalisar biyu na cikin ‘yan majalisa 26 da suka amince baki ɗaya da sanarwar tsige Gwamna Fubara da mataimakiyarsa.
Sai dai yanzu kuma sun canza shawara, sun ce suna bukatar a koma teburin tattaunawa ne domin samar da zaman lafiya mai dorewa, kamar yadda Vanguard ta kawo.
Majalisar dokokin Ribas ta koka
A wani labarin, kun ji cewa Majalisar Dokokin Jihar Rivers ta bayyana cewa ana yunkurin hana ta shirin ta a tsige Gwamna Siminalayi Fubara da Mataimakiyarsa.
Ta kuma samu sahihan bayanai cewa wasu mutane na neman umarnin kotu domin hana Majalisar aiwatar da ayyukanta na kundin tsarin mulki.
Majalisar ta kuma ambaci Sashe na 272(3) da 188(10) na Kundin Tsarin Mulki na 1999 waɗanda ke hana kotuna karɓar shari’o’in da suka shafi tsarin tsige shugabanni.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

