Tsohon Jigo a APC, Bugaje, Ya yi Wankin Babban Bargo ga Buhari, Tinubu da APC

Tsohon Jigo a APC, Bugaje, Ya yi Wankin Babban Bargo ga Buhari, Tinubu da APC

  • Daya daga cikin dattawan Arewa, Dr. Usman Bugaje ya soki tsarin karba-karba a shugabancin Najeriya
  • Tsohon 'dan majalisar ya bayyana gwamnatin APC tun daga Buhari har zuwa Tinubu a matsayin annoba ga kasa
  • A karkashin haka Hon. Bugaje ya bukaci a samar da shugabanci bisa cancanta ba bisa yanki ko kabilanci ba

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja -Jigo a kungiyar dattawan Arewa, Dr Usman Bugaje, ya ce tsarin shugabancin karba-karba a Najeriya bai haifar da wani ci gaba ba, sai dai kara jefa kasar cikin matsaloli.

A cewar Dr Bugaje, lokaci ya yi da za a daina mayar da shugabanci harkar yanki yanki, a mayar da hankali wajen samar da shugabanni masu kwarewa da kishin kasa.

Kara karanta wannan

Yadda gwamnatin tarayya ta nemi ba ni rashawar N5bn," Ɗan takarar shugaban ƙasa

Buhari
Dr Bugaje ya kushe mulkin APC a Najeriya. Hoto: Bashir Ahmed|Bayo Onanuga
Asali: Twitter

Bugaje a bayyana haka ne a wata tattaunawa da gidan talabijin na Arise, inda ya ragargaji gwamnatin jam’iyyar APC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa mulkin Muhammadu Buhari har zuwa na Bola Ahmed Tinubu, Najeriya ta kara tabarbarewa.

'Karba-karba ba mafita ba ce' - Bugaje

Bugaje ya bayyana cewa tsarin shugabancin karba-karba tsakanin Arewa da Kudu bai haifar da wani ci gaba ba tun bayan da aka fara amfani da shi shekaru 25 da suka gabata.

A cewarsa, duk da cewa ana bukatar shigar da kowa a harkar mulki, bai kamata a mayar da hankali kan yanki ko kabila ba, saboda hakan na hana samun shugabanni nagari.

“Mun gwada wannan tsarin na karba-karba, amma Najeriya na kara tabarbarewa. Ya kamata mu fara sabon tunani:”

- Dr Usman Bugaje

Bugaje ya ce gwamnatin APC annoba ce

Bugaje ya bayyana cewa gwamnatin APC tun daga mulkin Buhari har zuwa Tinubu ta jefa Najeriya cikin mawuyacin hali, inda ya ce sun kasa magance matsalolin da suka addabi kasar.

Kara karanta wannan

"An ba Tinubu gurguwar shawara," Ɗan Majalisa ya tona kura kuran da aka gano a ƙudirin haraji

“Mun sha fama da matsalolin shugabanni da ba su san abin da ya kamata su yi ba. Wadanda suka fi mai da hankali kan tara dukiya maimakon samar da ci gaba,”

- Dr Usman Bugaje

Bugaje ya kara da cewa manyan alamomin ci gaban kasa kamar ilimi, kiwon lafiya da tattalin arziki duk sun tabarbare. Ya ce dimokuradiyyar da ake yi a yanzu ta sabawa ainihin manufarta.

Maganar zaben shugabanni a Najeriya

Tsohon 'dan majalisar ya jaddada cewa Najeriya tana bukatar shugabanci na gari ba wai wanda za a rika zaben mutane bisa la’akari da yankin da suka fito ba.

“Babu wani yanki da ke da lasisin iya mulki fiye da wani. Akwai kwararru da dama a Najeriya daga sassan Kudu da Arewa da za su iya jagorantar kasar nan cikin basira,”

- Dr Usman Bugaje

Ya kara da cewa idan har ana son ci gaban kasa, to ya zama dole a dakatar da fifita yanki ko addini wajen zaben shugabanni.

Kara karanta wannan

APC na yi wa jam'iyyar adawa dauki dai-dai, dan majalisar PDP ya sauya sheka

Bugaje ya bukaci ‘yan Najeriya da su farka daga barci, su fara duba cancanta da nagarta a shugabanni ba wai yankin da suka fito ba.

A cewarsa, idan har ba a farka ba, to Najeriya za ta ci gaba da fuskantar koma baya, kuma hakan zai shafi kowa da kowa ba tare da la’akari da yankin da mutum ya fito ba.

'APC da PDP duk daya ne' inji Bugaje

Bugaje ya bayyana cewa ba APC ce ta gaza kawai ba, har da sauran jam’iyyun siyasa da ke Najeriya. Ya ce tun daga PDP zuwa APC babu wani canji na a zo a gani da aka samu.

“A matsayina na dan Najeriya, ba zan yarda da APC ko PDP ko wata jam’iyya ba. Duk suna da matsala iri daya. Muna bukatar sabon tsarin mulki da zai kawo shugabanni nagari,”

Kara karanta wannan

Manyan sarakuna 5 masu daraja da kotu ta tsige daga sarauta a cikin shekara 1

Dr Usman Bugaje

'Dan majalisa ya yi magana kan 2027

A wani labarin, kun ji cewa Dan majalisar tarayya daga jihar Zamfara, Aminu Jaji ya bukaci 'yan siyasa su daina magana kan takarar Bola Tinubu a 2027.

Hon. Jaji ya bayyana cewa yanzu lokacin ayyukan gina kasa ne ba maganar zabe mai zuwa da fara rikicin siyasa a Najeriya ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng