Ganduje Ya Kai Batun APC a gaban Attajirai, Ya Fadi Bukatarsa

Ganduje Ya Kai Batun APC a gaban Attajirai, Ya Fadi Bukatarsa

  • Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje na son ganin APC ta samu nasara a zaɓen gwamnan jihar Anambra
  • Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya buƙaci attajiran jihar da su yi amfani da dukiyarsu wajen gina jam'iyyar maimakon tarwatsa ta
  • Shugaban na APC ya bayyana cewa suna son gudanar da sahihin zaɓen fidda gwani a gwamna a jihar da jam'iyyar APGA ke mulki

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi muhimmin kira ga mambobin jam'iyyar a jihar Anambra.

Abdullahi Ganduje ya buƙaci mambobin jam’iyyar a jihar su yi amfani da dukiyarsu wajen bunƙasa jam’iyyar maimakon amfani da ita wajen tarwatsa ta.

Ganduje ya yi kira ga attajirai
Ganduje ya bukaci attajirai su gina APC a Anambra Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

Ganduje ya yi wannan kira ne a ranar Talata a Abuja yayin da ya karɓi baƙuncin wata ƙungiyar matasan APC mai suna 'Booth to Booth with Bola Tinubu', cewar rahoton jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan

"Gwamna da abokin takarar Atiku na roƙon a bari su shigo APC," Sanata ya ce babu wurinsu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wace buƙata Ganduje ya nema game da APC?

Ganduje ya yi wannan kiran ne gabanin zaɓen fidda gwani na gwamna da za a gudanar a ranar 8 ga watan Nuwamba, 2025 a jihar Anambra

"Ya kamata Anambra ta taimaka wajen samar da kyakkyawan yanayi. A matsayinmu na jam’iyya, idan muna son samun ingantaccen zaɓen fidda gwani a jihar, dole ne duk masu ruwa da tsaki su canja hali."
“Akwai matsaloli da dama kamar ƙararraki da umarnin kotu. Mun gaya musu cewa a wannan lokaci, ba za a ci gaba da tafiyar da harkoki kamar da ba."
"Mu tallafawa tsarin. Mun san suna da kuɗi sosai, amma bai kamata su yi amfani da kuɗinsu wajen tarwatsa jihar ba."
"Ya kamata su yi amfani da kuɗinsu wajen gina jihar, ba wajen tarwatsa ta ba. Ya kamata su yi amfani da kuɗinsu wajen gina APC domin ta samu nasara."
“Gaskiya, zan yi matuƙar farin ciki idan suka iya tsayar da ɗan takara ta hanyar cimma matsaya. Zan ba su lambar yabo."

Kara karanta wannan

2027: Masari ya taso masu son kawar da Tinubu a gaba, ya fadi makomarsu

- Abdullahi Umar Ganduje

Dangane da yadda zaɓen fidda gwanin zai kasance a jihar, Ganduje ya ce kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) zai zauna don tattauna batun tare da shugabannin jam’iyyar a jihar da sauran masu ruwa da tsaki kafin a yanke hukunci.

An buƙaci APC ta yi adalci?

Shugaban ƙungiyar, Iyke Madu, ya buƙaci kwamitin NWC ƙarƙashin Ganduje da ya zaɓi tsarin zaɓen fidda gwani na ƙato bayan ƙato a Anambra.

“Kafin babban zaɓe, dole ne a fara da zaɓen fidda gwani na jam’iyya. Mun zo nan ne don mu nemi wata alfarma, wato ku tabbatar da cewa an gudanar da zaɓen fidda gwani sahihi, na gaskiya da adalci a jihar Anambra."

- Iyke Madu

Jam'iyyar APC ta roƙi ƴan Najeriya

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar APC ta miƙa ƙoƙon bararta ga ƴan Najeriya kan zaɓen 2027 da ke tafe.

APC ta buƙaci ƴan Najeriya da ka da su yi kuskuren sake dawo da jam'iyyar PDP a kan madafun ikon ƙasar nan, duba da ɓarnar da ta tafƙa a shekara 16 da ta yi tana jagoranci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng