Rashin Cika Alkawarin Buhari Ya Jawo An Maka APC a Kotu, Ɗan Takara na Neman N110m
- Sunny Moniedafe, tsohon ɗan takarar APC, ya shigar da ƙara a kotu yana neman a mayar masa da N10m da ya biya na kudin fom a 2022
- Shari’ar Moniedafe ta gamu da cikas saboda rashin halartar alkalin kotu, Justice Yusuf Halilu, a jiya Talata, 21 ga watan Janairu
- Moniedafe ya bukaci kotu ta tilasta APC ta mayar masa da N10m cikin kwanaki bakwai da kuma diyyar N100m na kudaden yakin zabe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Tsohon ɗan takarar kujerar mataimakin shugaban APC na kasa (shiyyar Arewa), Sunny Moniedafe, ya kai karar jam’iyyar a kotu.
Sunny Moniedafe ya shigar da ƙarar ne a babbar kotun tarayya Abuja, yana neman a mayar masa da Naira miliyan 10 da ya biya na sayen fom ɗin takara a 2022.

Asali: Twitter
Tsohon dan takara ya maka APC a kotu
Amma, sauraron ƙarar da aka tsara yi a ranar Talata bai yiwu ba saboda rashin halartar Mai Shari’a Yusuf Halilu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shari’ar wadda aka shirya ci gaba da saurarenta a ranar Talata, ta gamu da cikas saboda rashin halartar alkalin kotun, Mai shari’a Yusuf Halilu, inji rahoton Punch.
A cikin ƙarar mai lamba FCT/HC/CV/2434/2024, Sunny Moniedafe ya bayyana cewa ya biya kudin fom din ne kafin babban taron APC na ranar 26 ga Maris, 2022.
Ya yi nuni da cewa ya biya zunzurutun kudi har Naira miliyan 10 da nufin tsayawa takarar kujerar mataimakin shugaban jam'iyyar na kasa a shiyyar Arewa.
Me ya faru da kudin takarar Moniedafe?
Sunny Moniedafe ya bayyana cewa a lokacin babban taron, shugabannin APC karkashin tsohon Shugaban kasa Muhammadu Buhari suka bukaci masu takarar su janye.
Ya ce akwai lokacin, mahukuntan APC sun yanke shawarar cewa kujerar mataimakin shugaban jam'iyyar za ta koma ga wani daga jihar Borno, yankin Arewa maso Gabas.
Moniedafe ya ce kafin babban taron, shugabannin jam’iyyar sun yarda za a fitar da dan takara guda daya kawai, shi ne dalilin umartar saurar su janye.
Ya ce a lokacin ne tsohon shugaban kasa, Buhari ya umarci a mayar wa waɗanda suka janye daga takarar N10m na kudin fom da suka saya.
"Na aikawa Buhari, Tinubu wasiku" - Moniedafe
Duk da haka, ya Moniedafe ce:
“Abin takaici, shugabannin sun saba alkawarin kuma sun ƙi dawo mun da N10m dina. Tun daga Maris din 2022 har zuwa lokacin shigar da wannan ƙara nake binsu a kan kudin."
Ya ƙara da cewa ya aika da wasiƙu zuwa ga manyan jami’an APC da shugabanni, ciki har da Buhari, tsohon shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari.
Sauran wadanda ya aikawa wasikar sun hada da shugaban kasa na yanzu Bola Tinubu da tsohon sshugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan da sauransu.
Moniedafe ya ce duk da waɗannan korafe korafen, tarin wasiƙun tare da tunatarwa game da maida kuɗin sun gaza cimma sakamakon da yake buƙata.

Kara karanta wannan
An gano abin da zai jefa 'yan Najeriya miliyan 13 a talauci a 2025, an gargadi gwamnati
Dan takarar na neman APC ta biya shi N120m
Tsohon dan takarar ya jaddada cewa a lokacin da aka ba da wannan umarnin, tsohon shugaban kasa Buhari ne yake matsayin jagoran APC.
Saboda haka, Moniedafe ya nemi kotu ta bayar da umarnin tilasta APC ta maido masa da N10m cikin kwanaki bakwai bayan hukuncin kotun.
Haka kuma, ya nemi a biya shi tara ta N100m a matsayin diyya kan kuɗaɗen da ya kashe a lokacin yakin neman zabensa na 2022.
A ƙarshe, ya nemi kotu ta bayar da duk wani umarnin da ta ga ya dace a cikin wannan yanayi.
2022: Mutane 169 suka yi takara a APC
A wani labarin, mun ruwaito cewa akalla mutane 169 aka tabbatar sun sayi fom na neman takarar mukamai daban-daban a jam’iyyar APC a shekarar 2022.
Mutane shida ne suka nemi kujerar babban mataimakin shugaban jam’iyya na kasa, ciki har da Sunny Moniedafe, Isa Yuguda, Yakubu Dogara da sauransu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng