An Fara Samun Baraka a APC kan Takarar Seyi Tinubu, Jiga Jigan Jam'iyyar Sun Ja Layi
- Yayin da ake ta ce-ce-ku-ce kan takarar ɗan shugaban kasa a Lagos, baraka ta kunno kai a jam'iyyar APC ta kasa
- Jigon APC, Joe Igbokwe ya ce kira na amincewa da Seyi Tinubu a matsayin gwamnan Lagos ya kawo rarrabuwa, yana mai cewa shugabanci na bukatar kwarewa
- Sai dai kusa a APC, Isaac Balami ya ce matasa kamar Seyi Tinubu suna da kwarewa da basira don samar da shugabanci mai kyau da cigaban jihar Lagos
- Balami ya ce tarihin shugabanci ya nuna cewa matasa sun fi dacewa wajen kawo sauyi da ingantaccen cigaba a siyasa da tattalin arziki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Ikeja, Lagos - Maganganu sun fara yawa kan tunkuda ɗan shugaban kasa, Seyi Tinubu ya nemi takarar gwamnan Lagos a 2027.

Kara karanta wannan
'Su bar kujerunsu': Atiku ga yan siyasa da ke sauya sheka, ya fadi hanyoyin gyara dimukraɗiyya
Hakan ya fara kawo rarrabuwar kawuna hatta a cikin jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya inda jiga-jiganta suka fara muhawara.

Asali: Facebook
Jigon APC ya soki takarar Seyi Tinubu a Lagos
Jigo a APC, Joe Igbokwe ya soki masu goyon bayan Seyi Tinubu don zama gwamnan Legas, kamar yadda Tribune ta ce.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce shugabanci yana bukatar kwarewa, ba ga masu karancin gogewa ba inda ya ce ana neman karkatar da hankalin Bola Tinubu ne.
Igbokwe ya kara da cewa wannan kira wani shiri ne na dauke hankali daga manufofin Shugaba Bola Tinubu.
Kusa a APC ya soki Igbokwe kan kalamansa
Sai dai kuma wani kusa a APC, Isaac Balami ya mayar wa Igbokwe martani kan kalamansa game da Seyi Tinubu.
Balami ya bayyana cewa zai jagoranci matasa da kungiyoyi daban-daban don nuna goyon baya ga Seyi Tinubu, yana mai cewa matasa na da rawar da za su taka wajen ci gaban jihar.
Tsohon dan jam'iyyar LP ya ce lokaci ya yi da za a watsar da mulkin tsofaffi domin ba matasa dama, cewar The Nation.
Balami ya ce tarihin duniya ya nuna cewa matasa sun fi dacewa wajen shugabanci inda ya ba da misalan Yakubu Gowon da ya zama shugaban kasa yana da shekaru 32.
Ya ce Emmanuel Macron ma ya zama shugaban Faransa yana da shekaru 39 inda ya ce Seyi Tinubu, wanda zai kai shekaru 42 a 2027, ya cancanci jagorantar Lagos.
Jigon APC ya fadi tasirin matasa a mulki
Balami ya bayyana cewa matasa na da damar canza al’amura, yana mai cewa amfani da shekaru, jinsi, ko asali wajen zaben shugabanni yana hana samun cancanta da fasaha.
Ya ce Seyi Tinubu ya cancanci shugabanci saboda irin gudummawar da yake bayarwa ta cigaban matasa da tattalin arzikin Lagos.
Dan APC ya ce kungiyarsa za ta goyi bayan Seyi Tinubu idan ya yarda ya tsaya takara, domin tabbatar da cewa shugabanci ya koma hannun matasa masu basira da kuzari.

Kara karanta wannan
'Neman gwamna ba zunubi ba ne': Kakakin Majalisa da aka tsige ya fadi dalilin taso shi a gaba
An fara tone-tone kan takarar Seyi Tinubu
Kun ji cewa wata kungiyar matasan jihar Lagos ta yi watsi da kiran Ministan Matasa, Ayodele Olawande, na cewa Seyi Tinubu ya dace ya zama gwamna a 2027.
Kungiyar ta yi zargin cewa Seyi Tinubu ba ɗan jihar ba ne, kuma akwai isassun matasa da dattawan jihar da suka cancanci wannan matsayin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng