PDP Ta Dulmuya a Matsala da Tsarin Gwamnoni Ya Rushe, Ta Rasa Madafa kan Rikicinta
- Rikici cikin PDP ya sake dagulewa yayin da ake hasashen shakku kan taron kwamitin zartarwa ta NEC
- Taron na NEC na cikin shakku, yayin da bangarorin kwamitin ayyuka na NWC suka rarrabu kan wa'adin rikon shugabanci na Umar Damagum
- Gwamnonin PDP sun bukaci a kira taron NEC kafin farkon watan Fabrairun 2025 amma rikice-rikice na cikin gida sun sake kunno kai
- Mai magana da yawun Damagum da Anyanwu, Ibrahim Abdullahi ya ce za su mutunta umarnin kotu, yayin da Ologunagba ya tsaya kan matsayinsa na kwamitin NWC
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Rikicin cikin gida na ci gaba da zama kalubale ga jam'iyyar PDP game da taron kwamitin zartarwa da ake shirin yi a Najeriya.
Zaman kwamitin NEC na jam'iyyar PDP ya shiga hali na rashin tabbas saboda rikici tsakanin bangarorin NWC.

Asali: Twitter
Rikici ya sake lalata sulhun jam'iyyar PDP
Daily Trust ta ce Kwamitin NWC, wanda ke da alhakin shirya tarukan NEC, yana fama da rikici kan wa'adin rikon shugabanci na Ambasada Umar Damagum.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na zuwa ne yayin da rikici kan mukamin sakatare ya sake lalata sulhu yayin da Damagum da Anyanwu suka zargi Ologunagba da gudanar da aiki ba tare da shawara ba.
Ibrahim Abdullahi, wanda aka zaba a matsayin mai magana da yawun Damagum, ya ce jam’iyyar za ta mutunta umarnin kotu akan tarukan NEC.
Ologunagba ya ce shi kadai ke da ikon fitar da sanarwa, yayin da wasu ke shirye-shiryen kiran taron NEC na watan Fabrairu.
A baya, rikicin ya kai ga dakatar da Umar Damagum, Debo Ologunagba da wasu jiga-jigan jam'iyyar mai adawa.
Amma sulhun da gwamnonin PDP suka yi ya kawo zaman lafiya na ɗan lokaci kadan wanda ake ganin ba zai dore ba.
Matsayar gwamnonin PDP kan taron NEC
A taron birnin Jos, gwamnonin PDP karkashin jagorancin Bala Mohammed sun bukaci a kira taron NEC kafin farkon Fabrairun 2025 domin tattaunawa da masu ruwa da tsaki.
Mohammed ya ce akwai bukatar warware matsalolin jam'iyyar da kuma shari'ar da ake yi domin samun jagorancin na gari, cewar rahoton Punch.
"Tsakanin watan Nuwamba zuwa Fabrairun 2025 ya kamata ya warware matsalolin shugabanci da shari’a a cikin jam’iyyar."
- Gwamna Bala Mohammed
An sanya taron NEC tun a watan Agustan 2024, amma aka dage zuwa Nuwamba, har daga bisani aka jingine ba tare da saka ranar karshe ba.
Jigon PDP ya kalubalanci jagorancin Damagum
Kun ji cewa kusa a PDP, Kola Ologbondiyan ya bayyana cewa Umar Damagum yana rike da kujerar mukaddashin shugaban jam’iyyar PDP na kasa ba bisa ka’ida ba.
Ologbondiyan wanda jigo ne a babbar jam'iyyar adawar ya kara da cewa wannan daya ne daga tarin matsalolin da su ka sanya PDP a gaba a yanzu.
Babban kusa a jam'iyyar ya yi zargin cewa wasu ƙungiyoyi daga waje suna ƙoƙarin tarwatsa PDP tare da mayar da ita reshe na jam’iyyar APC mai mulki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng