Shugaba a APC Ya Yi Zazzafan Martani ga El Rufa'i kan Hadaka da 'Yan Adawa

Shugaba a APC Ya Yi Zazzafan Martani ga El Rufa'i kan Hadaka da 'Yan Adawa

  • Jam’iyyar APC ta bayyana cewa ba ta damu da hadin kai da ake zargin Nasir El-Rufai da tawagar Atiku Abubakar da SDP sun kulla ba
  • Wani jigo a jam'iyyar APC ya ce irin taron da ake yi tsakanin ’yan adawa ba zai yi tasiri a siyasar Najeriya ba a zaben shekarar 2027
  • APC ta yi ikirarin cewa matakan da Bola Tinubu ya dauka sun fara nuna sakamako mai kyau ga kasar nan wajen habaka tattali

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Jam’iyyar APC ta bayyana cewa ba ta cikin damuwa game da rahotannin da ke nuna cewa Nasir El-Rufai na tattaunawa da SDP da wasu abokan tafiyar Atiku Abubakar.

Rahotanni sun nuna cewa El-Rufai ya hadu da shugabannin SDP da wasu manyan mutane daga tawagar Atiku Abubakar a wata ganawar sirri da aka yi a sakatariyar SDP a makon da ya gabata.

Kara karanta wannan

Abba ya yabi jami'i mai amana, kwamitin rabon kayan makaranta ya maido rarar N100m

Ganduje
APC ta yi martani kan ganawar El-Rufa'i da 'yan adawa. Hoto: Nasir El-Rufa'i|Salihu Tanko Yakasai
Asali: Facebook

Punch ta wallafa cewa ana zargin taron na daga cikin shirin hadin kai tsakanin manyan ’yan adawa domin kalubalantar mulkin shugaba Bola Ahmed Tinubu a shekarar 2027.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Martanin APC kan haduwar El-Rufai da SDP

Mataimakin shugaban APC a Kudu maso Gabas, Dr Ijeoma Arodiogbu, ya bayyana cewa jam’iyyar ba ta damu da irin tarurrukan ba domin ba za su cimma wani abu ba.

Shugaban ya ce,

“Ba ma jin tsoron wannan taro saboda mun san ba za su cimma wani abu ba.
El-Rufai yanzu yana cikin rudani a harkar siyasa, kuma yana neman yadda zai dawo da farin jininsa ne kawai.”

Hadakar ’yan adawa da tasirinta

Rahotanni sun nuna cewa tarurrukan da ake yi tsakanin El-Rufai, SDP, da wasu bangarori na tawagar Atiku sun hada da tsohon gwamnan Kano, Ibrahim Shekarau.

Amma Shugaban SDP na kasa, Shehu Gabam, ya musanta cewa suna da wata alaka ta siyasa da El-Rufai ko Atiku.

Kara karanta wannan

Gwamnoni 6 sun ajiye siyasa gefe, sun ɗauki matakin kare jihohinsu daga ƴan ta'adda

Ya bayyana cewa babban burinsu yanzu shi ne karfafa tsarin jam’iyyarsu domin samar da zabin da ya dace ga ’yan Najeriya.

Jawabin APC kan manufofin Bola Tinubu

Arodiogbu ya ce matakan da gwamnatin shugaba Tinubu ta dauka sun fara nuna sakamako mai kyau, musamman a bangaren rage dogaro da tallafin fetur da karfafa tattalin arziki.

“Mun cire tallafin fetur, kuma yanzu kasuwa ce za ta kayyade farashi.
"Wannan zai taimaka wajen rage matsalolin tattalin arziki da kuma kara samun kudin shiga ta hanyar fitar da fetur kasashen waje,”

Jigon jam'iyyar ya kara da cewa ’yan Najeriya za su fahimci muhimmancin matakan da gwamnatin Tinubu ta dauka domin inganta rayuwar al’umma a gaba kadan.

Za a ciyar da Afrika gaba - Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyaba cewa nahiyar Afrika na da dukkan abin da zai kawo mata cigaba.

Kara karanta wannan

Zargin ta'addanci: Tsohon hadimin Matawalle zai shaƙi iskar ƴanci bayan hukuncin kotu

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana haka ne yayin wata ganawa da shugaban kasar Rwanda a wani taro da suka halarta a kasar Qatar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng