'Sun Sha Bamban da Yan Siyasar Najeriya': Shugaban INEC Ya Yabawa Hukumar Zaben Ghana
- Shugaban hukumar INEC a Najeriya, Farfesa Mahmood Yakubu ya yabawa kasar Ghana kan yadda aka gudanar da zabe
- Farfesa Yakubu ya koka kan yadda yan siyasar Najeriya ke sauya sheka lokacin da suka ga dama ba kamar Ghana ba
- Wannan na zuwa ne bayan gudanar da zaben kasar cikin lumana a jiya Asabar 7 ga watan Disambar 2024
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Shugaban hukumar INEC a Najeriya (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu ya magantu kan zaben kasar Ghana.
Farfesa Yakubu ya bayyana sha’awarsa kan siyasar Ghana inda ya ce yan siyasa ba sa sauya sheƙa zuwa wata jam’iyya a duk zaɓen gama-gari kamar Najeriya.
Mahmood Yakubu ya yabawa siyasar kasar Ghana
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa tsohon shugaban ƙasar Ghana, John Dramani Mahama ya lashe zaɓen da aka gudanar a jiya Asabar 7 ga watan Disambar 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mahmood Yakubu ya yaba da tsarin gudanar da zaɓe a Ghana, musamman sababbin fasahohinsu da kuma zaman lafiyar siyasa.
Ya ce hakan ya taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da sahihin gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na 'yan majalisar dokokin ƙasar na 2024.
Farfesa Yakubu wanda ya sanya ido kan zaɓen tare da masu sa ido na Yiaga Africa, ya bayyana gamsuwarsa da zaman lafiyar siyasar Ghana.
Har ila yau, Farfesa Yakubu ya kuma yaba da daidaiton tsarin jam’iyyun siyasa da aminci ga masu zaɓe a ƙasar, cewar Punch.
Farfesa Yakubu ya fadi matsalar siyasar Najeriya
“A Ghana, ba kasafai ake ganin mutane suna sauya sheƙa daga wata jam’iyya zuwa wata ba a duk zaɓen gama-gari."
“Ya na kawo zaman lafiya, haka kuma yana ba magoya bayan jam’iyyun damar kasancewa tare da jam’iyyarsu tsawon shekaru.
"Ko jam’iyyar tana mulki ko tana hamayya, magoya bayanta suna tsayawa tsayin-daka wurin tabbatar da nasararta."
- Mahmood Yakubu.
Obasanjo ya caccaki shugaban INEC, Mahmood Yakubu
Kun ji cewa tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya caccaki shugaban INEC, Mahmood Yakubu kan abubuwan da suka faru a 2023.
Obasanjo ya ce akwai bukatar a kori Farfesa Yakubu da sauran jami’an INEC a matakin jiha da kananan hukumomi na kasar nan.
Asali: Legit.ng