An Kawo Gawar Tsohon Shugaban Majalisa, Sanatoci Sun Yi Masa Bankwana

An Kawo Gawar Tsohon Shugaban Majalisa, Sanatoci Sun Yi Masa Bankwana

  • Sanatoci a Najeriya sun yi bankwana da gawar tsohon shugabanta, Dr. Joseph Wayas a yau Alhamis a harabar Majalisar
  • Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio ya yi jimamin mutuwar Joseph Wayas, ya bayyana irin gudunmawar da ya bayar a siyasa
  • Wannan na zuwa ne bayan shafe shekaru uku da Wayas ya yi da mutuwa tun a ranar 30 ga watan Nuwambar 2021

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Majalisar Dattawa ta yi zama na musamman domin bankwana da gawar tsohon shugabanta.

Sanatocin sun yi bankwana da marigayi Joseph Wayas a yau Alhamis 28 ga watan Nuwambar 2024 a Abuja.

An kawo gawar tsohon shugaban Majalisar Dattawa a harabarta
Sanatoci sun yi bankwana da gawar marigayi Sanata Wayas. Hoto: The Nigerian Senate.
Asali: Facebook

Yaushe Sanata Wayas ya mulki Majalisar Dattawa?

Tribune ta ruwaito cewa Wayas ya rasu ne tun a ranar 30 ga watan Nuwambar 2021 kusan shekaru uku kenan zuwa yanzu.

Kara karanta wannan

Shettima, Jonathan da 'yan siyasa sun halarci birne matar gwamna, hawaye sun zuba

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Marigayi Dr. Wayas ya shugabanci Majalisar tun a Jamhuriya ta biyu lokacin mulkin marigayi Shehu Shagari daga shekarar 1979 zuwa 1983.

Dr. Wayas ya rasu ne yana da shekaru 80 a duniya inda aka shirya birne shi a karshen mako mai zuwa a jihar Cross River, cewar Vanguard.

Sanatoci sun yi magana kan marigayi Wayas

Mafi yawan sanatocin yayin bankwana da marigayin sun bayyana irin gudunmawar da ya bayar a bangaren siyasa.

Yayin da wasu suka tabbatar ba su taba haduwa da shi ba, wasu ko sun tabbatar da tuno wasu abubuwa game da shi lokacin suna yara.

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya yabawa marigayin inda ya ce ya kawo sauyi a Majalisar bayan dawowa mulkin dimukradiyya.

Akpabio ya fadi irin kalubalen da yan Majalisa a wancan lokaci suka fuskanta wurin tabbatar da dimukradiyya bayan shekaru na mulkin soja.

An yi bankwana da gawar Sanata Ubah

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kashe dattijo mai shekaru 85 bayan karɓar kudin fansa

Kun ji cewa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya halarci bikin bankwana da gawar marigayi Sanata da ya rasu.

An kawo gawar Sanata Ifeanyi Ubah cikin Majalisar Dattawa domin sanatoci su yi masa bankwana a birnin Abuja.

Wannan na zuwa ne bayan mutuwar Ubah da ke wakiltar Anambra ta Kudu a Burtaniya a watan Yulin 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.