Yadda Sarki Ya Fito Ƙarara Ya Goyi Bayan Ɗan Takarar Gwamnan APC
- Yan siyasa a jam'iyyu daban daban na cigaba da neman goyon bayan al'umma yayin da zaben gwamnan Ondo ke kara matsowa kusa
- Wani babban basarake a jihar Ondo, Oba Olufaderin Adetimehin ya nuna goyon baya ƙarara ga dan takarar APC, Lucky Aiyedatiwa
- Oba Olufaderin Adetimehin ya yi kira ga masu zabe a jihar Ondo su sanya kuri'u ga gwamna Lucky Aiyedatiwa a zaben jihar da za a yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Ondo - Gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa ya je yakin neman zabe masarautar Ile-Oluji a Ondo.
Mai martaba Oba Olufaderin Adetimehin ya karbi gwamnan kuma ya jaddada masa cewa zai samu nasara yayin zabe.

Asali: Twitter
Jaridar the Nation ta wallafa cewa gwamna Lucky Aiyedatiwa ya ce zai cigaba da dukkan ayyukan da ya fara a jihar idan ya samu nasara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan APC ya ziyarci fadar sarki
Gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa ya kai ziyarar yakin neman zabe masarautar Ile-Oluji a jihar Ondo.
Lucky Aiyedatiwa ya yi alkawarin cigaba da kawo ayyukan alheri a jihar Ondo idan ya samu nasara a karo na biyu.
Mai girma Lucky Aiyedatiwa ya kara da cewa duk wata matsala da ta taso a jihar zai yi kokarin magance ta.
Sarki ya goyi bayan ɗan takarar APC
Sarkin Ile-Oluji, mai martaba Oba Olufaderin Adetimehin ya bayyana cewa yana tare da gwamna Lucky Aiyedatiwa dari bisa dari.
Oba Olufaderin Adetimehin ya ce yana da tabbas a kan cewa Allah ne ya zabi gwamna Lucky Aiyedatiwa domin ya jagoranci Ondo.
"Idan aka sanar da sakamakon zabe, gwamna Lucky Aiyedatiwa zai tabbatar da cewa kiran da muke a zabe shi ba a fatar baki ya tsaya ba kawai."
- Oba Olufaderin Adetimehin
Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya fita yakin neman zabe ne tare da wasu jiga jigan jam'iyyar APC na jihar.
Ondo: Kusa a SDP ta koma APC
A wani rahoton, kun ji cewa gwamna Lucky Aiyedatiwa na jihar Ondo ya karbi wata kusa a jam'iyyar SDP ana daf da gudanar da zaɓe.
Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya karbi mataimakiyar dan takarar gwamna a jam'iyyar SDP, Susan Gbemisola Alabi ana shirin zaɓe.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng