Harajin Tsaron Yanar Gizo: Pantami Ya Magantu da CBN Ya Fitar da Sabuwar Sanarwa

Harajin Tsaron Yanar Gizo: Pantami Ya Magantu da CBN Ya Fitar da Sabuwar Sanarwa

  • Babban bankin Najeriya (CBN) ya janye umarnin da ya ba bankuna da cibiyoyin hada-hadar kudi na karbar harajin tsaron yanar gizo
  • Wannan harajin dai na tsaron yanar gizo ya jawo cece-kuce daga 'yan Najeriya yayin da wasu ke sukar bankin da ma gwamnatin kasar
  • A safiyar yau Litinin, tsohon ministan ministan tattalin arziki na zamani, Farfesa Isa Ali Pantami ya yi hamdaLah kan janye harajin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Tsohon ministan ministan tattalin arziki na zamani, Farfesa Isa Ali Pantami, ya yi magana bayan babban bankin Najeriya ya janye harajin tsaron yanar gizo.

Farfesa Isa Ali Pantami ya yi magana kan harajin CBN
Farfesa Isa Ali Pantami ya yi godiya ga Allah bayan CBN ya janye harajin tsaron yanar gizo. Hoto: @cenbank, @ProfIsaPantami
Asali: Twitter

Tsohon ministan ministan ya yi martanin ne a shafinsa na X.

Tun da fari, mun ruwaito cewa CBN ya umurci bankuna da cibiyoyin hada-hadar kudi da su rika karbar harajin kashi 0.5% kan duk hada-hadar kudin abokan hulda.

Kara karanta wannan

Mutanen Arewa sun taso Ministan Tinubu a gaba sai ya yi murabus daga kujerarsa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An yi adawa da harajin CBN

Sai dai wannan umarnin bai yi wa jama'ar kasar dadi ba, inda suka nuna adawa karara yayin da suke kalubalantar bankin kan bullo da tsarin alhalin 'yan kasar na fama da matsin tattali.

Mun ruwaito yadda majalisar wakilai ta ba CBN umarnin ya dakatar da aiwatar da wannan umarnin, yayin da Sanata Ali Ndume ya nuna kakaba harajin kuskure ne babba.

Dattawan Arewa kuwa, sun yi fatali da wannan harajin da bankin ya bullo da shi, inda suka nemi gwamnati ta sake tunani kan lamarin saboda halin da 'yan ƙasar ke ciki.

CBN ya janye harajin yanar gizo

Amma a sabuwar sanarwar da ya fitar, wadda jaridar The Nation ta wallafa, babban bankin kasar ya janye umarnin da ya ba bankuna na karbar wannan haraji na tsaron yanar gizo.

Kara karanta wannan

Yayin da Najeriya ke tangal tangal, Tinubu zai sake karbo bashin $2.25bn

Janye umarnin na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga Chibuzo A. Efobi, daraktan sashen kula da tsarin biyan kudi na CBN, da Haruna B. Mustafa, daraktan sashen tsare-tsaren kudi.

Duk da hakan, babban bankin ya yi nuni da cewa akwai yiwuwar ya sake yin nazari kan harajin domin bullo da sabuwar hanyar karbar kudaden tsaron yanar gizon.

“Alhamdu Lil Laah”: Pantami ya magantu

A safiyar yau Litinin, tsohon ministan, Farfesa Pantami ya yi martani kan wannan sabuwar sanarwar ta CBN.

Kamar yadda ya wallafa a shafinsa na X, Pantami ya ce:

“Alhamdu Lil Laah”.

Tinubu ya dakatar da harajin CBN

A baya, mun ruwaito cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya dakatar da CBN daga aiwatar da harajin 0.5% na tsaron yanar gizo da ta ba bankuna umarnin su karba.

Shugaban kasar ya ce ya damu da halin da 'yan Najeriya ke ciki kuma ba zai bari a kara musu wata wahala ba, inda ya nemi bankin ya yi wa tsarin kwaskwarima.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.