'Yan Daba Sun Yi Yunƙurin Kai Farmaki Fadar Gwamnatin Kano Yayin Rantsar da Ɗan Kwankwaso

'Yan Daba Sun Yi Yunƙurin Kai Farmaki Fadar Gwamnatin Kano Yayin Rantsar da Ɗan Kwankwaso

  • Wasu ƴan daba sun yi yunkurin kawo hargitsi a bikin rantsar da sabbin kwamishinoni ciki har da ɗan Kwankwaso a fadar gwamnatin Kano
  • SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyana cewa dakarun ƴan sanda sun yi nasarar cafke su ba tare da sun cimma burinsu ba
  • Kwamishinan ƴan sandan Kano ya ce duk wani zagayen ƴan jagaliya a muhimman wurare ya zo ƙarshe, rundunar za ta ɗauki matakai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta cafke wasu mutane takwas da ake zargi da yunkurin kawo cikas a bikin rantsar da sababbin kwamishinoni hudu a gidan gwamnatin Kano.

Lamarin dai ya faru ne a yayin bikin rantsarwar wanda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jagoranta a ɗakin taron majalisar zartaswa na fadar gwamnati.

Kara karanta wannan

Benue: Tashin hankali yayin da ƴan sanda suka ƙwace iko da sakateriyar APC

CP Gumel na jihar Kano.
An damƙe wasu ƴan daba 8 da suka yo yunkurin tada yamutsi a fadar gwamnatin Kano Hoto: Kano Police Command
Asali: Facebook

'Yan daba a gidan gwamnatin Kano?

Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya sanar da kama waɗanda ake zargin ranar Alhamis, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar sanarwar, wadanda ake zargin sun haifar da barazana ga tsaro a gidan gwamnati, lamarin da ya sa ‘yan sanda suka dauki matakin gaggawa.

CP ƴa gargadi ƴan daba a Kano

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, CP Usaini Gumel, ya gargadi duk wasu ‘yan daba, bata-gari da masu daukar nauyinsu da su nisanci harkokin gwamnati.

CP ya jaddada cewa jami'an tsaro ba za su yi ƙasa a guiwa ba wajen ɗaukar matakin daƙile duk wani yunƙuri na tada tarzoma da kawo cikas ga tsaro.

"Batun ƴan jagaliya da ke zagayawa a gidan gwamnati, sakatariyar Audu Bako da sauran ofisoshi ya zo ƙarshe," in ji Gumel.

Kara karanta wannan

Kasar Yarbawa: Kotu ta rufe masu fafutukar raba Najeriya bisa zargin cin amana

Yadda lamarin ya faru

Ya kuma bayyana cewa shugaban ƴan daba 8 da aka kama, wanda ya nuna bai saduda ba, shi ne ya jagoranci yaransa zuwa ɗakin taron da ake rantsarwar.

A cewarsa, yunkurin da yan daban suka yi ya ja hankalin yan sanda da ke sintiri a wurin, wanda nan take suka cafke su kuma suka ci gaba da sa ido.

An kuma gano cewa ƴan daban da aka kama magoya bayan wani ɗan siyasa ne da ke yunƙurin karya doka da oda, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Yan sanda sun karbe sakateriyar APC

A wani rahoton kun ji cewa jami'an rundunar ƴan sanda sun ƙara kwace iko da sakatariyar tsagin APC wanda Kwamared Austin Agede ke jagoranta a jihar Benue.

Rahoto ya nuna cewa tun da farar safiya ƴan sanda suka girke motocin su, suka toshe duk wata hanya ta shiga sakateriyar a Makurɗi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262