Gwamna Abba Ya Rantsar da Mustapha Kwankwaso da Wasu Kwamishinoni 3

Gwamna Abba Ya Rantsar da Mustapha Kwankwaso da Wasu Kwamishinoni 3

  • Mustapha Rabiu Musa Kwankwaso ɗan tsohon gwamnan jihar Kano ya samu muƙamin kwamishina a gwamnatin jihar Kano
  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya rantsar da Mustapha tare da wasu mutum uku a matsayin sababbin kwamishinoni a gwamnatinsa
  • Mustapha zai jagoranci ma'aikatar matasa da wasanni yayin da sauran mutum uku su ma aka ba su ma'aikatun da za su jagoranta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya rantsar da sababbin kwamishinoni huɗu a gwamnatinsa.

Daga cikin sababbin kwamishinonin da aka rantsar akwai Mustapha Rabiu Musa Kwankwaso, wanda ɗa ne a wajen jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso.

An rantsar Mustapha Kwankwaso
Mustapha Kwankwaso ya zama kwamishinan matasa na Kano Hoto: @Kyusufabba/@imranvashyr
Asali: Twitter

Sababbin kwamishinonin Abba

Kwamishinonin waɗanda aka rantsar a ranar Alhamis, 18 ga watan Afirilun 2024 an kuma ba su ma'aikatun da za su jagoranta.

Kara karanta wannan

'Yan daba sun yi yunƙurin kai farmaki fadar gwamnatin Kano yayin rantsar da ɗan Kwankwaso

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hadimin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, Ibrahim Adam, shi ne ya sanya batun rantsar da kwamishinonin a shafinsa na Facebook.

Sababbin kwamishinonin da aka rantsar sun haɗa da Mustapha Rabiu Musa Kwankwaso, Abduljabbar Garko, Shehu Aliyu Yarmedi da Adamu Aliyu Kibiya.

Rantsar da su da aka yi domin kama aiki na zuwa biyo bayan amincewar da majalisar dokokin jihar ta yi da naɗin da aka yi musu bayan ta tantance su.

Waɗanne ma'aikatu za su jagoranta?

Mustapha Rabiu Musa Kwankwaso ya zama sabon kwamishinan wasanni da matasa na jihar Kano.

Ga jerin sauran kwamishinonin da ma'aikatun da za su jagoranta:

1. Abduljabbar Garko - ƙasa da safiyo

2. Shehu Aliyu Yarmedi - ayyuka na musamman

3. Adamu Aliyu Kibiya - kasuwanci da masana’antu

Legit Hausa ta tuntuɓi wani mazaunin jihar Kano, mai suna Ibrahim Zulkiful, wanda ya yi wa kwamishinonin fatan nasara da addu'ar Allah ya ba su ikon sauke nauyin da ke kansu.

Kara karanta wannan

Gwamnoni sun ɗauki matsayi kan batun sauya shugaban PDP na ƙasa a taron NEC

Ya nuna jin daɗinsa kan yadda gwamnati mai ci ta jawo matasa take damawa da su a cikin harkokin mulki.

A kalamansa:

"Ina yi musu fatan alkhairi musamman yanzu da aka sanya matasa a ciki. Insha Allah muna yi musu kyakkyawan zato za su yi abin da ya dace."
"Insha Allah za a samu sauyi sosai tun da an sanya matasa a ciki, ba kamar a baya ba idan za a bada kwamishina sai a ɗauko ɗan shekara 50 ko 60."

An tura sunan Mustapha Kwankwaso zuwa majalisa

A baya Legit Hausa ta kawo rahoto cewa gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya sake tura sunayen mutane huɗu majalisar dokokin jihar domin tantance su.

Mai girma Abba Yusuf ya tura sunayen zuwa majalisar ne domin tantance su a matsayin ƙarin kwamishinoni a jihar.

Ɓatun naɗa ɗan Kwankwaso kwamishina

A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya ce ya naɗa Mustapha ɗan Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso a matsayin kwamishina saboda ya cancanta.

Gwamna Abba ya bayyana cewa Mustapha Kwakwanso yana daga cikin haziƙan matasan da suka yi aiki tuƙuru domin samun nasarar kafa gwamnatinsa a Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel