Jam'iyyar NNPP Ta Dakatar da Gwamma Abba Kabir Na Jihar Kano? Gaskiya Ta Bayyana

Jam'iyyar NNPP Ta Dakatar da Gwamma Abba Kabir Na Jihar Kano? Gaskiya Ta Bayyana

  • Jam'iyyar NNPP ƙarƙashin jagorancin Ahmed Ajuji ta musanta dakatar da gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf
  • Muƙaddashin shugaban NNPP na ƙasa ya ce waɗanda suka dakatar da Abba Kabir ƴan barkwancin siyasa ne da ke neman suna
  • Tun farko dai tsagin NNPP karkashin shugabancin Major Agbor ya dakatar da Gwamna Abba na tsawon watanni shida

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Kwamitin gudanarwa (NWC) na New Nigeria People’s Party (NNPP) ta ƙasa ya musanta dakatar da gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf.

NWC ya bayyana cewa babu wani dalili da zai sa a dakatar gwamnan daga jam'iyar NNPP, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Jam'iyyar NNPP ta musanta dakatar da gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Idan ba ku manta ba a ranar Talata, tsagin NNPP karƙashin jagoranci Major Agbor ya sanar da dakatar da gwamnan Kano na tsawon watanni shida.

Kara karanta wannan

Baɗaƙalar N80bn: Gwamnatin Tinubu ta yi magana kan rikicin Yahaya Bello da EFCC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ɗauki wannan matakin ne saboda gwamnan ya gaza bayyana a gaban kwamitin ladabtarwa domin kare kansa kan zargin yi wa dokokin NNPP karan tsaye.

Sakataren tsagin jam'iyyar na ƙasa, Ogini Olaposi ne ya sanar da dakatar da Gwamna Abba Kabir Yusuf a yayin wani taron manema labarai a Abuja.

Abba a NNPP: Menene sahihancin dakatarwar?

Da yake mayar da martani, mukaddashin shugaban NNPP na kasa, Dr. Ahmed Ajuji, ya bayyana cewa gwamnan cikakken mambam jam’iyyar ne na gaskiya.

Yayin hira da manema labarai a Abuja ranar Alhamis, Ajuji ya ce:

"Gwamna Abba Kabir cikakken mamba ne kuma mai kishin NNPP wanda ya kai matsayin jakadan NNPP, yadda ya ɗauko shugabanci da nasarorin da ya samu a Kano abin alfahari ne gare mu.
"Saboda haka babu wani dalili da zai sa mu dakatar da shi, a taƙaice ma dai jam'iyyar NNPP ba ta dakatar da gwamnan mu ɗaya tilo ba.

Kara karanta wannan

Gwamnoni sun ɗauki matsayi kan batun sauya shugaban PDP na ƙasa a taron NEC

NNPP ta caccaki tsagin Agbor

Ajuji ya caccaki masu ikirarin dakatar da gwamnan Kano, inda ya kira su da ƴan barkwancin siyasa, ƴan amshin shata da kuma masu neman suna saboda an yi watsi da su, rahoton Leadership.

Muƙaddashin shugaban NNPP na ƙasa ya ce waɗannan tsirarun mutane su ne a baya suka shigar da ƙararraki da dama a gaban kotun suna neman a ba su shugabanci jam'iyya.

Ina makomar Ganduje a APC?

Mun kawo muku rahoton cewa jam'iyyar APC ta jaddada cewa Dakta Abdullahi Umar Ganduje na nan daram a matsayinsa na shugaban jam'iyyar na ƙasa.

Mai magana da yawun APC, Felix Morka, ya ce ba za su yi aiki da umarnin kotun farko ba, amma suna tare da hukuncin babbar kotun tarayya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel