Kasar Yarbawa: Kotu ta Rufe Masu Fafutukar Raba Najeriya Bisa Zargin Cin Amana

Kasar Yarbawa: Kotu ta Rufe Masu Fafutukar Raba Najeriya Bisa Zargin Cin Amana

  • Wata kotun Majistare dake zamanta a Ibadan ta bayar da umarnin tisa keyar wasu mutane 29 gidan gyaran hali da tarbiyya bayan gurfanar da su gabanta
  • Tun da fari, masu fafutukar sun yi yunkurin kai hari gidan gwamnatin jihar Oyo tare da yi wa sakatariyar gwamnati da'ira dama kafa tutarsu
  • Ana tuhumarsu da laifuffukan cin amanar kasa, shiga da makami cikin jama'a, mallakar makami ba bisa ka'ida ba, da kuma shiga cikin haramtacciyar kungiya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Oyo, Ibadan-Babban kotun Majistare dake Iyaganku a Ibadan, Olabisi Ogunkanmi ya bayar da umarnin garkame wasu mutum 29 da ake zargi da fafutukar kafa kasar Yarabawa ta Oduduwa nation.

Kara karanta wannan

Tuhumar rashawa: Shari'ar gwamnatin Kano da Abdullahi Ganduje ta gamu da cikas

Jami'an rundunar yan sandan jihar Oyo ne suka cafke mutanen lokacin da suka yiwa sakatariyar jihar da'ira, kana suka dasa tutar kasar Yarabawar da suke fafutukar sai an kafa.

kotun ta aike da mutanen gidan gyaran hali
Kotu ta daure masu fafutukar kafa kasar yarabawa a Ibadan Hoto: Getty images
Asali: Facebook

Daga cikin wadanda aka kama akwai wata matashiya da mata guda biyar, inda aka same su dauke da muggan makamai, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yarbawa: Ana zarginsu da laifin cin amana

A rahoton The Guardian, rundunar yan sandan kasar nan ta gurfanar da masu fafutukar kafa kasar Yarabawa da laifufuka da dama ciki har da na cin amanar kasa.

Sauran laifukan sun hada da hada kai wajen cin amanar kasa, shiga haramtacciyar kungiya, shiga cikin jama’a rike da makamai, da laifin mallakar makami.

Daga cikin irin makaman da aka kama masu fafutukar da su akwai bindigu, adduna, wukake sai kuma layu.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta yi barazanar kwace lasisin rijiyoyin mai kan rashin biyan haraji

“Za mu kafa kasar Yarabawa,” Masu fafutuka

Gamayyar Kungiyar Yarabawa ta Yoruba World Congress mai dauke da kungiyoyi 107 , ta ce a shirye ta ke ta kafa kasar Yarabawa cikin kwanciyar hankali ba tare da zub da jini ba.

Shugaban kungiyar, Farfesa Banji Akintoye wanda ya bayyana hakan ya ce sun fara tafiyar ne da kungiyoyi 45, amma yanzu maganar ta yi nisa.

Ya ce sun daɗe suna fafutukar kafa kasar Yarabawa kuma gamayyarsu ta duƙufa don ganin yarabawa sun samu matsayin da ya dace da su a tsakanin ƙasashe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel