Majalisa Ta Ɗauki Sabon Mataki a Shirinta Na Tsige Mataimakin Gwamna, Ta Faɗi Muhimmin Dalili 1

Majalisa Ta Ɗauki Sabon Mataki a Shirinta Na Tsige Mataimakin Gwamna, Ta Faɗi Muhimmin Dalili 1

  • Majalisar dokokin jihar Edo ta sauya salo a yunƙurinta na tsige Philip Shaibu daga kujerar mataimakin gwamna
  • A zaman ranar Litinin, shugaban majalisar ya ce za su buga labarin shirinsu na tsige Shaibu a jaridu tun da ya ƙi karɓan sanarwa daga kotu
  • A makon da ya gabata majalisar ta fara bin matakan sauke Shaibu daga kujerarsa, lamarin da ya haddasa zanga-zanga daga mutane

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Edo - Majalisar dokokin jihar Edo ta ci gaba tattauna batun tsige mataimakin gwamnan jihar Edo, Kwamared Philip Shaibu.

Majalisar ta bayyana cewa zata sauya salo wajen sanar da Shaibu yunkurinta na tsige shi daga kan kujerar mataimakin gwamnan, Channels tv ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda da makiyaya ne ke jawo wahalhalun da ake sha a Najeriya, inji fasto Ayodele

Kujerar Shaibu na tsaka mai wuya a Edo.
Alamu na nuna Shiabu ka iya rasa kujerar mataimakin gwamnan Edo Hoto: Comrade Philip Shaibu
Asali: Facebook

Kakakin majalisar dokokin jihar Edo, Blessing Agbebaku, ne ya bayyana hakan yayin zaman majalisar na ranar Litinin (yau), 11 ga watan Maris, 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, Shaibu ya ki amincewa da sanarwar tsige shi da aka aike masa daga kotu ta hannun ma'aikatan DHL.

Wace hanya majalisar za ta bi wajen tsige Shaibu?

Agbebaku ya ƙara da cewa tun da ya ƙi amsar takardar sanarwan, a yanzu za a wallafa sanarwar shirin tsige mataimakin gwamnan a jaridun ƙasar nan.

Idan baku manta ba, a makon da ya shige ne majalisar dokokin ta fara shirin tsige Shaibu daga kujerar mataimakin gwamna biyo bayan rigingimun da suka dabaibaye PDP.

Shugaban masu rinjaye na majalisar, Charity Aiguobarueghian, ya ce mambobi 21 daga cikin 24 sun goyi bayan takardar ƙarar tsige Shaibu mai ɗauke da kwanan watan ranar 5 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Matasa da mata sun ɓarke da zanga-zanga kan yunƙurin majalisa na tsige mataimakin gwamna

Ya tabbatar da cewa adadin ‘yan majalisar da suka rattaba hannu kan takardar sun cika sharaɗin kashi biyu cikin uku da ake bukata kamar yadda kundin tsarin mulkin kasa ya tanada.

Ya kara da cewa, an shigar da karar ne bisa zargin mataimakin gwamnan da zabga karya da tona asirin gwamnatin jihar Edo, The Cable ta ruwaito.

Alaƙa dai ta yi tsami tsakanin Gwamna Godwin Obaseki da mataimakinsa, Shaibu bayan zaɓen fidda ɗan takarar PDP a zaɓen gwamnan Edo mai zuwa.

Gwamnatin Dikko za ta taimaki talakawa

A wani rahoton na daban Gwamnatin jihar Katsina ƙarƙashin Malam Dikko Raɗda ta shirya ciyar da mutane 2,166,000 masu ƙaramin karfi a tsawon kwanakin watan Ramadan.

Ranar Litinin, 11 ga watan Maris, 2024, Musulmai a Najeriya da wasu sassan duniya suka tashi da azumin watan Ramadan bayan ganin jinjirin wata ranar Lahadi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel