Janar ya Tsefe Gaskiya, Ya Fito da Abubuwan da Ke Kawowa Sojoji Cikas a Yaki

Janar ya Tsefe Gaskiya, Ya Fito da Abubuwan da Ke Kawowa Sojoji Cikas a Yaki

  • Wani kwamandan sojojin Najeriya, Manjo Janar Olufemi Oluyede ya bayyana irin matsalolin da suke kawo musu cikas a cikin aikisu
  • Manjo Janar Oluyede ya ce akwai bukata ta musamman wurin magance matsalolin domin samun nasara wurin yaki da ta'addanci
  • Shugaban sojojin Najeriya, Laftanal Janar Taoreed Lagbaja ya bayyana wa sojojin kan yadda za su yi kokarin magance matsalolin

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Kwamandan rundunar sojojin Najeriya, Manjo Janar Olufemi Oluyede, ya bayyana abubuwan da suke kowa musu cikas kan yaki da ƴan ta'adda a Najeriya.

Nigerian Army
Shugaban sojojin Najeriya ya ce za a magance matsalolin da sojoji ke fuskanta. Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: UGC

Matsalolin da sojoji ke fuskanta a yau

Manjo Janar Oluyede ya lissafa amfani da tsofaffin kayan aiki, karancin ma'aikata da rashin samar da walwalar sojoji a matsayin manyan abubuwan da suke kawo musu koma baya.

Kara karanta wannan

"Babu laifin Tinubu": Mataimakin kakakin majalisa ya magantu kan matsin tattali

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya yi jawabin ne a yayin taron wani horon sojoji na musamman a barikin soja da ke Jaji a jihar Kaduna, cewar rahoton Daily Trust.

Duk da haka shugaban sojan ya yabawa kokarin shugaban rundunar sojin ta kasa, wurin magance matsalolinsu.

Jami'in ya ce shugaban nasu yana kokari wurin ganin dukkan matsalolin da za su zama musu barazana an magance su.

Jawabin shugaban sojojin Najeriya

Da yake jawabi a wurin horon, shugaban sojojin Najeriya, Laftanal Janar Taoreed Lagbaja ya ce dukkan sojojin da aka tura fagen daga za su cigaba da samun kula ta musamman.

Laftanal Janar Lagbaja ya tabbatar musu da cewa kokarin da suke yi a wurin kare Najeriya ba zai tafi a banza ba.

Shugaban ya kuma yi kira ga sojojin da aka bawa horon wurin yin aiki yadda ya kamata da bin doka da oda.

Kara karanta wannan

Shugaban majalisa ya fadi wanda ya 'jawo' tabarbarewar tattalin arziki lokacin Buhari

Game da horon da aka musu kuma ya ce lalle horo yana da muhimmanci sosai musamman wurin yin nasara a fagen yaki, cewar jaridar Daily Post.

A karshe ya ce za su cigaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki wurin tabbatar da cewa sojoji suna samun kulawa da ta dace a Najeriya.

Sojoji sun hallaka yan ta'adda da dama

A wani rahoton, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun samu nasara kan ƴan ta'adɗa masu tayar da ƙayar baya a jihohin Borno da Kaduna bayan sun yi artabu.

A jihar Borno dakarun sojojin sun hallaka wani ɗan ta'adda tare da ceto wani yaro da suka sace a ƙaramar hukunar Nganzai ta jihar, sun kuma kwato wasu da dama a Kaduna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel