Majalisa Za Ta Tunbuke Mataimakin Gwamna a Karshen Mulkin PDP

Majalisa Za Ta Tunbuke Mataimakin Gwamna a Karshen Mulkin PDP

  • Mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu na shirin rasa kujerarsa bayan majalisar dokokin jihar ta fara shirin tsige shi
  • Majalisar dai ta aika da takardar fara shirin tsige Shaibu inda zai mayar da martani kan zarge-zargen da ake masa cikin kwanaki bakwai
  • Mataimamin gwamnan dai ya samu matsala da Gwamna Godwin Obaseki tun bayan da ya nuna aniyarsa ta yin takarar gwamnan jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Edo - A ranar Laraba ne majalisar dokokin jihar Edo ta sanar da fara shirin tsige mataimakin gwamnan jihar, Philip Shaibu.

An dai fara zaman majalisar ne da karfe 11:30 na safiyar Laraba, 6 ga watan Maris 2024, a harabar majalisar da ke birnin Benin, babban birnin jihar.

Kara karanta wannan

Kano: Gwamna Abba ya yi muhimman nade-nade a kananan hukumomin jiharsa

Ann fara shirin tsige Shaibu
Majalisar dokokin jihar Edo ta fara shirin tsige Philip Shaibu Hoto: Philip Shaibu
Asali: Facebook

Ana sa ran mataimakin gwamnan zai mayar da martani cikin nan da kwanaki bakwai kan zarge-zargen da ake masa, cewar rahoton NTA Network.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wata majiya daga gidan gwamnatin jihar bayyana cewa ƴan majalisa 22 daga cikin 24 sun sanya hannu kan takardar tsige Shaibu, wanda hakan ya sanya dole daga ƙarshe sai ya rasa muƙaminsa.

Jaridar The Nation ta ce fara shirin tsige Shaibu shi ne na baya-bayan nan a rikicin da ya ɓarke tsakaninsa da gwamnan jihar Godwin Obaseki.

Edo: Meya haddasa rikicin Obaseki v Shaibu?

Rikicin na su dai ya fara ne tun bayan da mataimakin gwamnan ya sanar da aniyarsa ta yin takarar gwamnan jihar a zaɓe mai zuwa.

Rikicin na su ya ƙara ƙamari bayan da aka gudanar da zaɓen fitar da gwanin gwamna na jam'iyyar PDP a jihar.

Kara karanta wannan

Gwamna Makinde ya fadi dalilin da ya sa jam'iyyar PDP ta rasa wata babbar jiha a hannun APC

Obaseki yana goyon bayan wani lauya mazaunin Legas, Asue Ighodalo, wanda ya lashe zaɓen fidda gwanin ɗan takarar jam’iyyar PDP na gwamna da aka gudanar a filin wasa na Samuel Ogbemudia, da ke birnin Benin.

Shaibu ya bayyana kansa a matsayin halastaccen ɗan takarar gwamnan jam'iyyar PDP, bayan ya lashe zaɓen fidda gwanin da ɓangarensa ya shirya.

Ƙungiyar NYCN Ta Yi Magana Kan Shirin Tsige Shaibu

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar matasan Najeriya ta (NYCN) reshen nahiyar Turai, ta yi magana kan shirin tsige mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu.

Ƙungiyar ta hannun shugabanta na ƙasar Sweden, kwamared Collins Idahosa, ta gargaɗi Gwamna Godwin Obaseki kan shirin tsige mataimakin gwamnan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel