Matasa da Mata Sun Ɓarke da Zanga Zanga Kan Yunƙurin Majalisa Na Tsige Mataimakin Gwamna

Matasa da Mata Sun Ɓarke da Zanga Zanga Kan Yunƙurin Majalisa Na Tsige Mataimakin Gwamna

  • Matasa maza da mata sun ɓalle da zanga-zanga a kan yunkurin majalisar dokoki na tsige mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu
  • Masu zanga-zangar sun gargaɗi PDP ta dakatar da shirin tsige Shaibu domin za su iya haɗa kan jama'a su juya mata baya a zaɓe mai zuwa
  • Shugaban PDP na Edo, Tony Aziegbemi, ya ce suna kokarin warware rikicin cikin ruwan sanyi amma ba zasu iya hana majalisa aikinta ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Edo - Ɗaruruwan matasa, maza da mata sun yi zanga-zanga a Jattu, mahaifar mataimakin gwamnan jihar Edo, Kwamared Philip Shaibu.

Yayin zanga-zangar da suka yi ranar Alhamis, sun yi kira ga majalisar dokokin Edo ta dakatar da shirinta na tsige mataimakin gwamnan, wanda ta fara ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Majalisa za ta tunbuke mataimakin gwamna a karshen mulkin PDP

Mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu.
Edo: Mata da Matasa Sun Barke da Zanga-Zanga Kan Shirin Tsige Shaibu Hoto: Rt. Hon. Comrade Philip Shaibu
Asali: Facebook

Sun bayyana cewa ci gaba da kokarin tsige Mista Shaibu daga kujerar mataimakin gwamna, ba zai yi wa jam'iyyar PDP dadi ba yayin da take shirin tunkarar zaɓe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masu zanga-zangar sun zagaya wasu manyan tituna a Jattu inda daga bisani suka karƙare a babbar mahadar Utokwe, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Menene buƙatar masu zanga-zangar?

Sun yi kira ga kwamitin gudanarwa na jihar da na ƙasa (NWC) na jam'iyyar PDP su shiga tsakani game da yunkurin majalisa na raba Shaibu da kujerarsa.

Daya daga cikin jagororin zanga-zangar, Mellow Oshiomah, ya ce sun damu da tsawon lokacin da aka ɗauka ana rigima tsakanin shugabannin jam’iyyar a jihar Edo.

Bisa haka, ya bukace su da su rungumi zaman lafiya, su sulhunta da juna domin maslahar PDP, cewar rahoton Leadership.

Sauran wadanda suka yi jawabai daga cikin masu zanga-zangar sun hada da, Aminu Umosor, Gafata Emmanuel da Haija Anetu Momodu.

Kara karanta wannan

NYCN ta tsoma baki kan yunƙurin tsige mataimakin gwamnan PDP, ta faɗi mafita 1 tak

Sun ce za su hada kan al’ummar jihar da kuma PDP domin su yaƙi jam’iyyar a zaɓe mai zuwa idan har aka ci gaba da shirin tsige Shaibu daga matsayin mataimakin gwamnan Edo.

Sai dai masu zanga-zangar sun yi kira ga ‘yan majalisar da su guji duk wani yunkuri na tsige mataimakin gwamnan domin jihar ta ci gaba da zama lafiya.

Ba zamu iya hana majalisa tsige Shaibu ba - PDP

Da aka tuntuɓe shi, shugaban PDP na Edo, Tony Aziegbemi, ya ce yayin da suke ƙoƙarin lalubo hanyoyin da za a magance rikicin cikin ruwan sanyi, ba za su hana majalisar gudanar da ayyukanta ba.

Ya ce:

"Jam'iyyar PDP tana kaunar zaman lafiya kuma tana kokarin sasanta komai amma ba abu ne da zamu fito mu faɗa wa duniya muna yin kaza da kaza ba.
"Majalisa kuma ba zamu dakatar da ita daga gudanar da ayyukanta kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada ba."

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Ministan Tinubu ya fadi dalili 1 da ya sa mutanen yankinsa ba za su yi zanga-zanga ba

Ko meyasa majalisa ta fara shirin tsige Shaibu?

A wani rahoton kuma Yayin da ake shirin tsige mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu, Majalisar dokokin jihar ta lissafo laifukan da Shaibu ya yi.

Majalisar a jiya Laraba 6 ga watan Maris ta fara shirin tsige mataimakin gwamnan kan zargin bankada sirrin gwamnatin jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel