"Tana Dauke da Kwayoyin Cututtuka": Hanyoyin da za Ku Kori 'Tsaka' daga Gidajenku

"Tana Dauke da Kwayoyin Cututtuka": Hanyoyin da za Ku Kori 'Tsaka' daga Gidajenku

A mahangar mutane da dama, tsaka ba ta da lahani, sau tari ana kallonta matsayin abar hana kwari zama a gida.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Igbo suna kiranta Agu Uno, a ƙasar Hausa kuma suna kiranta Tsaka, yayin da ake kiranta da Ọmọ onílé a harshen Yorùbá.

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Sai dai kuma a 'yan kwanakin nan, ana ta samun rahoton yadda Tsaka ke haddasa gobara ko kuma jefa cututtuka a jikin mutane wanda ke kai ga ajalin wasu.

Ko a Disambar 2022, mun ruwaito yadda wasu mutum shida 'yan gida daya suka mutu sakamakon cin abincin da Tsaka ta fada a ciki.

Hanyoyin da za ku kori Tsaka daga gidajenku
Hana Tsaka zama a gidaje zai kare mutane daga kamuwa da cututtuka da barazanar gobara. Hoto: Nando Vidal
Asali: Getty Images

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

BOUESTI: Jami'a ta kori ɗalibai mata 2 kan bidiyon da ya fito, ƴan sanda sun fara bincike

A mahangar bincike, Tsaka na zama haɗari ga mutane. Sau da yawa suna ɓoyewa a cikin gidaje yayin da kuma suke ɗauke da cututtuka kamar 'Salmonella', The Guardian ta ruwaito.

"Tsaka ba ta kisa nan take" - Onah

Eugene Onah, malamin dabbobi da nazarin halittu a jami'ar Najeriya, ya ce:

"Mutum ba zai mutu kai tsaye ba saboda Tsaka ta fada cikin abincin da ya ci.

“Sai dai kasancewar tana ɗauke da ƙwayoyin cuta da yawa a cikin bakinta, yiwuwar kamuwa da cutar 'bacteria' yana da yawa."

Kare gidanka daga annobar Tsaka

An tattaro cewa Tsaka na lalata kadarori ta hanyar bata bango da tauna wayoyin wuta wanda ke iya haddasa gobara. Domin hana Tsaka zama a gidanka, dole ka dauki matakai.

Ga waɗanda ke neman hanyar kare gidajenku daga waɗannan halittun, ga wasu hanyoyi guda biyar da za su iya hana Tsaka zama a gidanku.

1. 'Sai bango ya tsage...'

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 13 a Abuja, sun nemi N900m kudin fansa

Abu na farko da za ku fara yi shi ne toshe duk wasu ramuka ko kafofi da kuka san Tsaka da sauran kwari za su iya shiga dakunanku, Bahaushe ya ce "sai bango ya tsage Kadangare ke shiga."

Hatta kofofi ko tagunan da aka san basa rufewa 'ruf' akwai bukatar a gyara su, wannan zai taimaka Tsaka ba za ta samu kofar shigowa cikin gidajenku ba.

2. Yi amfani da bawon ƙwai

Bawon ƙwai na daya daga hanyoyin korar Tsaka cikin sauki domin suna kallon bawon a matsayin wani abu da ka iya kai masu farmaki, a cewar shafin wikihow.

Ka ajiye bari biyu-biyu na bawon ƙwai a lunguna da mashigar dakuna, sannan a rika canja su akalla bayan mako biyu ko uku domin kara ba Tsaka tsoro.

3. Yi amfani da tafarnuwa

Ba wai iya ga mutane ne kawai 'kamshi' ko ace 'warin' tafarnuwa ke takura mawa ba, hatta Tsaka ba ta kaunar warin tafarnuwa.

Kara karanta wannan

Miyagu sun tafka ɓarna, sun yi garkuwa da fasinjojin jirgin ruwa a Najeriya

Kamar yadda aka yi wa bawon ƙwai haka za a ajiye tafarnuwa a lunguna da mashigar dakuna da duk inda ake tunanin Tsakar na bi ta wuce, hakan zai kore ta da wuri-wuri.

4. Yi amfani da albasa

Warin albasa kamar na tafrnuwa, yana takurawa Tsaka, cikin kankanin lokaci yake korarta daga waje.

Ka yayyanka albasa ka ajiye a inda kasan tsaka na iya boyewa kamar wuraren da ke da dumi ko duhu wanda hankali bai cika kaiwa ba.

5. Yi amfani da maganin kashe kwari

Jaridar Tribune Online ta ruwaito cewa idan har ana so a yi wa Tsaka lahani, to a fara kawar da kwarin da take farautarsu a matsayin abinci ta hanyar fesa maganin kwari a dakuna da lungunan gida.

Idan ya zamana cewa Tsaka ba ta samun abinci a dakunan gidajenku, dole ne ta bar gidan ta nemi inda kuma za ta rika samun abincin. A rika fesa maganin kwari akai akai.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari kauyen Kaduna, sun kashe mutane da dama

6. Tsaftar muhalli

Mafi akasarin lokuta, Tsaka na mayar da muhallin da ba shi da tsafta a matsayin gurin zamanta. Yawan ajiye tarkace a waje daya na jawo wannan halitta ta zauna.

A dakuna girka abinci kuwa, akwai bukatar a daina tara kwanuka ko tarkace a waje daya, a rika ware komai tare da kife kwanuka da kuma rufe kayayyakin abinci.

Abin lura: Hanyoyin kare Tsaka daga gidaje na da dama, sai dai wadannan shida da muka lissafa a sama, za su taimaka kwarai wajen ganin an kori wannan halitta daga gidaje.

Tsire da lemu ya kashe mutum 7

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito yadda cin naman tsire da lemo ya yi ajalin mutum bakwai 'yan gida daya.

An tattaro cewa Mista Jessey, mai gidan ne ya siyo tsiren a garin Umuahia inda ya kawo wa iyalansa suka kwashi gara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel