Gwamnan PDP Ya Kunyata Mataimakinsa a Wurin Taro a Bainar Jama'a, Alaka Ta Kara Tsami Tsakaninsu

Gwamnan PDP Ya Kunyata Mataimakinsa a Wurin Taro a Bainar Jama'a, Alaka Ta Kara Tsami Tsakaninsu

  • Yayin da alaka ke kara tsami tsakanin Gwamna Obaseki da mataimakinsa, Shaibu, rikicin ya sauya salo a yanzu
  • A jiya ne Obaseki ya ki mika hannu ga mataimakin nasa yayin da ya zo su gaisa a jihar Bayelsa yayin rantsar da Gwamna Diri
  • Wannan na zuwa ne yayin da alaka ke kara tsami tsakanin Shaibu da mai gidansa Obaseki kan neman takara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Edo - Rikici tsakanin Gwamna Godwin Obaseki da Mataimakinsa, Philip Shaibu ta sauya salo.

Gwamnan ya ki gaisawa da Shaibu a wani faifan bidiyo yayin taron rantsar da gwamnan Bayelsa, Diri Douye a birnin Yenagoa.

Kara karanta wannan

Murna yayin da gwamnan APC ya fara raba kayan tallafi na biliyan 5 ga mabukata

Gwamnan PDP ya kunyata mataimakinsa a wurin wani taro yayin alaka ke kara tsami
Gwamna Obaseki ya ki gaisawa da mataimakin a wurin taro. Hoto: Godwin Obaseki, Philip Shaibu.
Asali: Twitter

Mene Gwamna Obaseki ya yi ga mataimakinsa?

Idan ba a mantaba, a jiya ne aka rantsar da Gwamna Douye Diri a matsayin gwamnan jihar a karo na biyu bayan nasara a zabe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin taron a birnin Yenagoa, Gwamna da sauran manyan baki suna zaune lokacin da Shaibu ya zo don gaisawa da su.

Bayan Shaibu ya gaisa da dukkan sauran bakin, da ya iso kan Obaseki sai ya ki mika masa hannu inda kawai ya yi kwana da hannunsa.

Wannan na zuwa ne yayin da alaka ke kara tsami tsakanin Shaibu da mai gidansa Obaseki.

Mene silas rikicin siyasa a tsakaninsu?

Hakan bai rasa nasaba da neman kujerar da Shaibu ke yi wanda a fili Obaseki ya nuna ba ya goyon bayansa.

Har ila yau, an tabbatar da cewa Obaseki ya na da dan takarar da ya ke inda Shaibu ke ganin ya ci amanarsa saboda rashin goyon bayansa.

Kara karanta wannan

Kano: Hankalin Kwamishinoni ya tashi bayan wa'adin da Abba Kabir ya ba su ya cika, bayanai sun fito

Rikicin na sake dagulewa ne yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben gwamnan jihar a karshen wannan shekara.

Jama'a da dama sun soki gwamnan da cewa ya na siyasa cike da gaba wanda hakan bai dace ba siyasance.

Hidimar Obaseki ta yi murabus

Kun ji cewa Hadimar Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo a bangaren kula da kokarin ma'aikata ta yi murabus daga kujerarta.

Sarah Ajose-Adeogun ta yi murabus din ne yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben jihar a karshen wannan shekara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel