Kano: Ka Kunyata 'Yan Sha Miyar Siyasa, NNPP Ta Magantu Kan Nasarar Abba Kabir, Ta Ba Shi Shawara

Kano: Ka Kunyata 'Yan Sha Miyar Siyasa, NNPP Ta Magantu Kan Nasarar Abba Kabir, Ta Ba Shi Shawara

  • Jami'yyar NNPP ta yi martani bayan nasarar da dan takararta a zaben gwamnan Kano, Abba Kabir ya yi
  • Jami'yyar a yankin Kudu maso Yamma ta ce wannan nasara ta bai wa 'yan sha miyar siyasa kunya
  • Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin jami'yyar a yankin, Kilamuwaye Badmus ya fitar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Jami'yyar NNPP a yankin Kudu maso Yamma ta taya Gwamna Abba Kabir samun nasara a Kotun Koli.

Jami'yyar ta ce nasarar ta kawo karshen 'yan shan miyar siyasa da ke neman ruguza abin da jama'ar Kano su ka zaba.

NNPP ta magantu bayan nasarar Gwamna Abba Kabir a Kotun Koli
Jami'yyar NNPP ta yi martani kan hukuncin Kotun Koli a zaben Kano. Hoto: Abba Kabir.
Asali: Facebook

Mene NNPP ta ce kan nasarar Abba Kabir?

Kara karanta wannan

Kano: Abba Gida-Gida ya aika muhimmin sako ga Gawuna bayan hukuncin Kotun Koli

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin jami'yyar a yankin, Kilamuwaye Badmus ya fitar a yau Asabar 13 ga watan Janairu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Badmus ya ce 'yan shan miyar an kore su ne daga NNPP shi ne suka hada kai don kawo cikas a shari'ar zaben Kano, cewar Tribune.

Ya ce mafi yawansu sun sha kunya ganin yadda Kotun Koli ta yarfar da su da kuma mayar da su marasa amfani a siyasa.

Sakon NNPP ga Gwamna Abba Kabir

Sanarwar ta ce:

"Mun gode wa Allah da nasarar Gwamna Abba Kabir a Kotun Koli a jiya Juma'a 12 ga watan Janairu.
"Wannan nasara a kunyata 'yan sha miyar siyasa da suke munafurtar NNPP ga APC a tunaninsu za a sallame su.
"Sun yi iya kokarinsu don bata wa Abba Kabir suna amma ba su yi nasara ba duk da karairayin da su ke a kansa."

Kara karanta wannan

Bayan na Kano, Kotun Koli ta raba gardama kan shari'ar gwamnan PDP a Arewa, ta fadi dalili

Jami'yyar har ila yau, ta bukaci gwamnan ya ci gaba da aikin alkairi don inganta rayuwar al'ummar jihar Kano kamar yadda ya saba, Newstral ta tattaro.

Abba Kabir ya yi martani bayan hukuncin Kotu

A wani labarin, Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya yi martani bayan sanar da hukuncin Kotun Koli a jiya.

Abba ya ce ya ji matukar farin ciki ganin yadda mutane ke murna saboda nasarar da ya samu.

Ya ce wannan hukunci ya tsame shi daga zargin badakala a zaben da aka gudanar a watan Maris kan cewa ya yi almundahana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel