Yanzun Nan: Gawar Gwamnan APC da Allah Ya Yi Wa Rasuwa Ta Iso Najeriya, Hotuna Sun Bayyana

Yanzun Nan: Gawar Gwamnan APC da Allah Ya Yi Wa Rasuwa Ta Iso Najeriya, Hotuna Sun Bayyana

  • Gawar marigayi gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ta iso gida Najeriya yau Jumu'a, 5 ga watan Janairu, 2024
  • An dawo da gawar marigayi tsohon gwamnan ne daga ƙasar Jamus, inda ya rasu bayan fama da doguwar jinya
  • Legit Hausa ta tattaro cewa Akeredolu ya kwanta dama ne a ranar Laraba, 27 ga watan Disamba, 2023 bayan fama da cutar daji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Akure, jihar Ondo - Gawar marigayi tsohon gwamnan jihar Ondo, Arakunrin Oluwarotimi Akeredolu, SAN, CON, ta iso gida Najeriya.

Wannan na kunshe a wani saƙo da aka wallafa a shafin X wanda aka fi da Twitter, inda aka sauko da gawar daga cikin jirgin sama.

Kara karanta wannan

Cikakken sunayen tsaffin gwamnonin Ondo 5 da suka mutu a tarihi banda mutum 1 tak da ya tsira

An dawo da gawar gwamnan APC da ya mutu Najeriya.
Gawar Gwamna Rotimi Akeredolu Ta Iso Najeriya Domin Binne Shi, Hotuna Sun Bayyana Hoto: Oluyemi Fasipe AICMC
Asali: Twitter

An ga matar da tsohon gwamnan ya mutu ya bari, Betty, na tsaye tana kallon sauko da gawar mamacin cikin yanayin ban tausayi da alhini.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An tattaro cewa gawar tsohon gwamnan ta iso Najeriya daga ƙasar Jamus da misalin ƙarfe 3:39 na yammacin yau Jumu'a, 5 ga watan Janairu, 2024.

Idan baku manta ba Legit Hausa ta kawo muku rahoton cewa Gwamna Akeredolu ya rasu ne ranar Laraba, 27 ga watan Disamba, 2023 a ƙasar Jamus bayan dogon lokaci yana jinyar cutar daji.

A watan Satumba, 2023 Gwamnan ya dawo Najeriya bayan shafe tsawon watanni uku yana hutun jinya da rashin lafiya a ƙasar Jamus da ke nahiyar turai.

Sai dai bayan haka kuma marigayi gwamnan ya sake ɗaukar hutun tafiya jinya bisa umarnin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, inda ya miƙa ragamar mulki ga mataimakinsa, Lucky Aiyedatiwa.

Kara karanta wannan

Uwar gidan shugaban kasa Remi Tinubu ta ziyarci iyalan Akeredolu, bayanai sun fito

Yadda Gwamna Akeredolu ya cika a Jamus

Bayan labarin mutuwar ta yaɗu, iyalan marigayin sun bayyana cewa Gwamna Akeredolu ya mutu ne a cikin bacci lokacin da yake jinyar ciwon kansa a asibitin Jamus.

Akeredolu Jnr ne ya sanar da mutuwar mahaifinsa a hukumance a wani rubutu da ya wallafa a Facebook a madadin iyalai.

Mutum uku da aka sace sun mutu a kokarin gudowa

A.wani rahoton na daban Wasu mutum uku da suka faɗa hannun masu garkuwa da mutane sun mutu a kokarin gudowa daga sansanin yan bindiga.

Sanata mai wakiltar Kogi ta Yamma a majalisar dattawa, Sunday Karimi, ne ya bayyana haka a Lokoja ranar Jumu'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel