Cikakken Sunayen Tsaffin Gwamnonin Ondo 5 da Suka Mutu a Tarihi Banda Mutum 1 Tak da Ya Tsira

Cikakken Sunayen Tsaffin Gwamnonin Ondo 5 da Suka Mutu a Tarihi Banda Mutum 1 Tak da Ya Tsira

A ranar Laraba 27 ga watan Disamba, gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu ya rasu a kasar Jamus bayan fama da jinya.

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Da yammacin ranar ce kuma aka rantsar da mataimakinsa, Lucky Aiyedatiwa a matsayin gwamnan jihar.

Jerin tsaffin gwamnonin Ondo da suka mutu a jihar
Dukkan tsaffin gwamnonin sun mutu banda Olusegun Mimiko. Hoto: Olusegun Mimiko, Rotimi Akeredolu.
Asali: UGC

Jerin gwamnonin da suka mutu

Wannan mutuwa ta Akeredolu ya sa muka binciko muku dukkan tsaffin gwamnonin jihar da suka rasu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga cikin wadanda aka zaba kujerar gwamnan jihar duk sun rasu banda Olusegun Mimiko wanda ya mulki jihar daga 2009 zuwa 2017.

Legit Hausa ta jero muku cikakken sunayensu tsaffin gwamnonin:

Kara karanta wannan

Akeredolu: Fitaccen malamin addini ya fadi wanda zai zama gwamnan Ondo a 2024

1. Pa Michael Adekunle Ajasin (1979-1983)

Ajasin ya hau karagar mulki a matsayin gwamnan jihar Ondo a shekarar 1979.

Marigayin ya gina jihar musamman ta bangaren ilimi da harkar noma da bunkasa yankunan karkara.

Ajasin ya riga mu gidan gaskiya ya na da shekaru 78 bayan ya sha fama da jinya.

2. Bamidele Olumilua (1992-1993)

Bayan mulkin soja na dan karamin lokaci, Bamidele ya karbi ragamar mulkin jihar Ondo, cewar The Nation.

Ya samu tasgaro a mulkinsa saboda matsalolin siyasa inda ya rasu a 2020 ya na da shekaru 80.

3. Cif Adebayo Adefarati (1999-2003)

Adefarati ya hau mulkin jihar bayan sojoji sun dawo da mulkin farar hula a shekarar 1999.

Tsohon gwamnan ya rasu bayan fama da cutar da ba a bayyana ba ya na da shekaru 76, cewar TheCable.

4. Dakta Olusegun Agagu (2003-2009)

Agagu ya mai da hankali wurin inganta harkar ilimi da lafiya da kuma bunkasa tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Aiyedatiwa: Jerin hadiman gwamna da suka yi murabus daga muƙamansu bayan mutuwa ta gitta

Rahotanni sun tabbatar cewa tsohon ministan ya rasu a 2013 a Legas ya na da shekaru 65 bayan ya fadi.

5. Olusegun Mimiko (2009-2017)

Mimiko shi ne kadai tsohon gwamnan jihar da ya rage a raye inda dukkan sauran suka rasu.

Tsohon gwamnan da aka fi sani da ‘Iroko’ kafin zama gwamna ya rike mukamin kwamishinan lafiya har sau biyu.

6. Rotimi Akeredolu (2017-2003)

Rotimi ya rasu ne a kasar Jamus bayan fama da cutar daji da ta dade a jikinsa na tsawon lokaci.

Ya na daf da kafa tarihin kammala wa’adinsa biyu a kan mulki kaman Mimiko mutuwa ta dauke shi ya na da shekaru 67.

Akeredolu ya rasu

A wani labarin, tsohon gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeradolu ya riga mu gidan gaskiya.

Rotimi ya rasu ne a ranar Laraba 27 ga watan Disamba a kasar Jamus bayan ya sha fama da jinya mai tsawo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel