Kanin Ministan Tinubu da Ke Neman Gadar Kujerar Yayansa Ya Janye Daga Takarar, an Bayyana Dalili

Kanin Ministan Tinubu da Ke Neman Gadar Kujerar Yayansa Ya Janye Daga Takarar, an Bayyana Dalili

  • Austin Umahi, kanin tsohon gwamnan jihar Ebonyi ya janye takarar neman kujerar sanatan Ebonyi ta Kudu
  • Umahi ya bayyana haka ne a yau Juma’a 29 ga watan Disamba bayan nuna sha’awar gadar kujerar yayan nashi
  • Wannan na zuwa ne bayan Umahi ya nuna sha’awar tsayawa takara don gadar kujerar sanatan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ebonyi – Kani ga tsohon gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi ya janye daga takarar sanatan Ebonyi ta Kudu.

Austin Umahi ya janye takarar ce bayan jam’iyyar APC ta tura kujerar zuwa karamar hukumar Oniocha.

Kanin tsohon gwamnan APC ya janye neman gadar kujerar yayansa
Austin ya janye neman takarar kujerar yayansa, Dave Umahi. Hoto: Dave Umahi, Austin Umahi.
Asali: Facebook

Wane mataki Austin Umahi ya dauka?

Umahi ya dauki matakin ne a yau Juma’a 29 ga watan Disamba bayan nuna sha’awar gadar kujerar yayan nashi, cewar The Nation.

Kara karanta wannan

2024: Kwanaki 2 da mutuwar gwamna, Lucky ya manta da shi ya ziyarci Tinubu kan wani babban dalili

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Francis Nwifuru shi ya ba da umarnin tura kujerar zuwa Oniocha wanda hakan ya tilasta Umahi janyewa wanda ya fito daga karamar hukumar Ohaozara.

Tsohon gwamnan jihar ya ajiye kujerar sanatan ne bayan Shugaba Tinubu ya ba shi mukamin Minista a gwamnatinsa.

Tinubu ya nada Umahi ne Ministan Ayyuka tun farkon hawanshi kujerar mulkin kasar a watan Mayu.

Wace sanarwa Austin ya fitar kan takarar?

Acikin wata sanarwa da aka fitar, iyalan Umahi sun bayyana janyewar Austin wanda ke da haske da an bar kujerar a yankinsa.

Sanarwar ta ce Austin Umahi ya janye ne daga takarar don ba da dama da tabbatar da an samu zaman lafiya, cewar TheCable.

Sanarwar ta ce:

“Muna sanar da ku cewa a ranar 28 ga watan Disamba, iyalan marigayi Joseph Umahi Nwaeze da ke Umunaga a karamar hukumar Ohaozora sun yi zaman kan kujerar sanata.

Kara karanta wannan

Majalisar UN tayi maganar rayuka 190 da aka kashe a Najeriya, Tinubu yana hutu a Legas

“Iyalan sun fahimci hukuncin jam’iyyar APC a jihar wurin tura kujerar zuwa karamar hukumar Oniocha."

Kanin tsohon gwamna ya nuna sha’awar kujerar yayansa

A wani labarin, kanin tsohon gwamnan jihar Ebonyi, Austin Umahi ya nuna sha’awar tsayawa takatar sanata a mazabar Ebonyi ta Kudu.

Umahi ya na son gadar kujerar tsohon gwamnan jihar, Dave Umahi bayan ya ajiye kujerar saboda mukamin Minista.

Asali: Legit.ng

Online view pixel