Take Take ta Tabbata: Kanin Minista Yana Neman Sanatan da Danuwansa Ya Ajiye a Majalisa

Take Take ta Tabbata: Kanin Minista Yana Neman Sanatan da Danuwansa Ya Ajiye a Majalisa

  • Kanin Sanata Dave Umahi ya ce zai so ya gaji ‘danuwansa da ya bar kujerarsa a majalisar dattawa
  • A makon nan ‘danuwan tsohon Sanatan wanda yanzu ya zama Minista ya shaidawa duniya burinsa
  • Austin Umahi zai so ya samu takarar Majalisa domin ya wakilci mutanen Kudancin jihar Ebonyi

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Ebonyi - Austin Umahi ‘danuwa ne ga tsohon gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi, ya nuna sha’awar zama Sanatan Ebonyi ta Kudu.

A wani rahoto da aka samu a Punch, an fahimci Austin Umahi yana harin kujerar da yayansa, Dave Umahi ya bari a majalisar dattawa.

Umahi
Austin Umahi da David Umahi @Imranmuhdz/Dave Umahi
Asali: UGC

Umahi sun maida Ebonyi gidan gado?

Nan da farkon 2024 hukumar INEC za ta shirya zabe domin cike gibin kujerun da ake da su, daga ciki akwai na Sanatan kudancin Ebonyi.

Kara karanta wannan

Kanin ministan Tinubu ya yunkuro don gadar kujerar yayansa ta sanata, ya fadi dalili

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutanen kudancin jihar Ebonyi sun rasa wakilci a majalisar dattawa da Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya ba Dave Umahi kujerar Minista.

Tsohon gwamnan ya karbi tayin Ministan ayyuka na tarayya, ya hakura da matsayinsa na Sanata da aka zabe shi a shekarar 2023.

Austin Umahi ya dace da Sanata

Austin Umahi zai so ya gaji wannan kujera kamar yadda ya yi wa ‘yan jarida jawabi a garin Abakaliki ranar Litinin, 25 ga watan Disamba.

Umahi ya shaidawa manema labarai ya cancanci ya rike wannan matsayi a majalisa. Tun tuni ake tunanin yana hangen matsayin.

Idan ya samu takara kuma jama’a su ka zabe shi, Umahi ya yi alkawarin mutanen yankin kudancin Ebonyi za su samu wakilci mai kyau.

"Tsarin damukaradiyya na hakika shi ne kurum hanyar da za a amince da ita wajen fito da Sanatan mazabar.

Kara karanta wannan

Abin da ya sa farin jinin Tinubu yake raguwa tun da ya gaji Buhari - Jigon APC

Zan yi wa mutane bakin kokarina wajen wakilci, saboda na samu gogewa a harkokin kasuwanci da siyasa."

- Austin Umahi

Rahoton ya ce Austin Umahi shi ne Darekta Janar na yakin neman zaben APC a takarar gwamna da aka yi a Ebonyi a zaben da ya gabata.

‘Danuwan Ministan ayyukan ya ce APC ta tsaida cewa daga karamar hukumar da ya fito watau Ohaozara za a tsaida ‘dan takaran Sanatansu.

Austin Umahi: Ka fi Gwamna a Ebonyi?

An taba rahoto Solomon Semaka yana cewa Sanata Dave Umahi ya kai sunan ‘danuwansa na jini, Austin Umahi domin a ba shi mukami.

A lokacin da Umahi yayi shekaru takwas yana gwamna, ana zargin da ‘danuwansa aka juya akalar mulkin jihar Ebonyi kamar hakkin gidansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng