SDP Ta Yi Maja da PDP, NNPP da Sauransu Don Yakice Tinubu? Jam’iyyar Adawa Ta Fadi Gaskiya

SDP Ta Yi Maja da PDP, NNPP da Sauransu Don Yakice Tinubu? Jam’iyyar Adawa Ta Fadi Gaskiya

  • Jam'iyyar SDP ta nesanta kanta daga wata kungiyar hadaka da ke kokarin aiki tare don fatattakar Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu
  • SDP ta bayyana yunkurin da ake zargin ana yi a matsayin dabaru na rashin kishin kasa kuma wanda baya bisa tsarin damokradiyya
  • Jam'iyyar ta ce tana sane da gagarumin makircin wanda ya samu goyon bayan manyan yan adawa da wasu kamfanoni masu zaman kansu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

FCT, Abuja - A ranar Juma'a, 8 ga watan Disamba, jam'iyyar Social Democratic Party (SDP) ta yi watsi da rade-radin yin hadaka da wasu jam'iyyun adawa don raba Shugaban kasa Bola Tinubu da kujerarsa.

Kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto, Alfa Mohammed, kakakin kungiyar, ya bayyana cewa "jam'iyyar SDP ta kuduri aniyar yin hulda mai kyau da gwamnatin Tinubu na tsawon shekaru uku masu zuwa."

Kara karanta wannan

Ana tsaka da kiran a tsige shi, an gano Wike yana rawar wakar Tinubu a ofishin Gbajabiamila

Jam'iyyar SDP ta nesanta kanta daga masu hadewa Tinubu kai
SDP Ta Yi Maja da PDP, NNPP da Sauransu Don Yakice Tinubu? Jam’iyyar Adawa Ta Fadi Gaskiya Hoto: @SegunShowunmi, @NGRPresident
Asali: Twitter

Babu tattaunawar yin maja a SDP - Gabam

Jam'uyyar ta sha alwashin kin sanya kanta a duk wani shirye-shirye da ke nufin kawo cikas ga gwamnatin jam'iyyar APC mai mulki ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Arise TV ta kuma rahoto matsayar SDP. Da yake magaba a baya-bayan nan, Shehu Gabam, shugaban jam'iyyar na kasa, ya bayyana cewa babu wata tattaunawa ta yin maja a cikin jam'iyyar.

Saboda haka, SDP ta hannun Mohammed ta bukaci yan Najeriya da su kasance masu tunani "ta fuskar farfagandar da za ta iya cutar da su".

Wani bangare da sanarwar na cewa:

"Jam'iyyar SDP na burin fayyace matsayinta dangane da rade-radin cewa tana cikin masu yin hadaka a kan gwamnatin Shugaban kasa Tinubu.
"SDP ta nisanta kanta daga irin wannan salo na siyasar rashin kishin kasa da kuma rashin bin tafarkin dimokradiyya."

Kara karanta wannan

Wata sabuwa yayin da aka zargi Tinubu da haddasa rikicin siyasa a Kano

Atiku ya magantu kan shirin maja

A baya Legit Hausa ta rahoto cewa jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta ƙasa ta nesanta kanta da jita-jitar haɗa maja da wasu jam'iyyun adawa.

Idan baku manta ba, an tattaro cewa PDP da New Nigerian Peoples Party (NNPP) sun fara yunkurin curewa wuri ɗaya domin tunkarar babban zaɓe mai zuwa a 2027.

Asali: Legit.ng

Online view pixel