APC Ta Nuna Yatsa Kan Wanda Take Zargi da Kai Mummunan Farmaki Gidan Kwamishinan Zabe a Kogi

APC Ta Nuna Yatsa Kan Wanda Take Zargi da Kai Mummunan Farmaki Gidan Kwamishinan Zabe a Kogi

  • Kungiyar kamfen din APC ta yi zargin cewa yan daban jam'iyyar SDP ne suka kai farmaki gidan kwamishinan zaben na jihar Kogi
  • Kingsley Femi Fanwo na APC wanda ya yi jawabi a taron manema labarai, ya yi ikirarin cewa yan barandar sun kuma yi yunkurin kona gidan gwamnatin jihar Kogi
  • Saboda haka APC ta bukaci jami'an tsaro da su dauki mataki kan halin dan takarar gwamnan SDP a zaben da za a yi ranar 11 ga watan Nuwamba, Murtala Ajaka

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Lokoja, jihar Kogi - Jam'iyyar APC ta daura alhakin harin da yan bindiga suka kai gidan kwamishinan zabe na jihar, Gabriel Longpet kan jam'iyyar Social Democratic Party (SDP).

Kara karanta wannan

Tsige Abba Gida Gida: An kama mutum 7 kan hukuncin Kotun Daukaka Kara, cikakken bayani

Kamar yadda jaridar Punch ta rahoto, Kingsley Fanwo, kakakin kungiyar kamfen din APC, wanda ya yi jawabi a wani taron manema labarai a ranar Juma'a, 1 ga watan Disamba, ya ce yan bindihar sun kuma yi yunkurin kona gidan gwamnatin jihar Kogi.

APC ta zargi jam'iyyar SDP da kai hari gidan kwamishinan zabe a jihar Kogi
APC Ta Nuna Yatsa Game da Wadanda Suka Farmaki Kwamshinan Zabe a Kogi Hoto: Kingsley Femi Fanwo, INEC Nigeria
Asali: Facebook

'SDP na tafiyar da gungun masu aikata laifuka' - APC

A cewar Fanwo, dan takarar gwamna na jam'iyyar SDP, Murtala Yakubu Ajaka, da magoya bayan SDP sun nuna kwakkwarar shaidar cewa su mutane ne masu rikici kuma ya kamata a rike su kan abun da ya faru a gidan kwamishinan zaben.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar The Nation ta nakalto jam'iyyar ta APC tana cewa:

"Ba mu da matsala da ba tawagar lauyoyi damar duba takardu da kayayyaki. Al'ada ce. Amma ba za mu bari kowani dan siyasa mai shan jini ya yi wadaka da ainahin hukuncin da mutanen Kogi suka yanke ba.

Kara karanta wannan

APC ta mayarwa Sule Lamido martani: Har yanzu kura-kuren PDP muke gyarawa

"Muna ganin ta'asar da dan takarar SDP da aka kayar da gungun masu aikata laifinsa suka aikata. Sun shigo da yan daba cikin Kogi daga jihohi masu makwabtaka."

A halin da ake ciki, jaridar Blueprint ta rahoto cewa jam’iyyar APC ta bukaci yan sanda, hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), da sauran hukumomin tsaro da su gaggauta cafke Ajaka.

Yan bindiga sun farmaki gidan kwamishinan zabe

A baya mun ji cewa yan bindiga sun kai mummunan hari gidan kwamishinan zabe a Lokoja da ke jihar Kogi.

Legit ta tattaro cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 3:30 na daren yau Juma’a 1 a watan Disamba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng