Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Farmaki Gidan Kwamishinan Zaben Jihar Kogi, Bayanai Sun Fito

Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Farmaki Gidan Kwamishinan Zaben Jihar Kogi, Bayanai Sun Fito

  • Wasu ‘yan bindiga dauke da muggan makamai sun kai mummunan hari gidan kwamishinan zabe a jihar Kogi
  • Lamarin ya faru ne a daren Juma’a 1 ga watan Disamba da misalin karfe 3:30 na tsakar dare a Lokoja da ke jihar
  • Hukumar zabe mai zaman kanta, INEC ta bayyana wannan mummunan labari a shafinta na sada zumunta

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kogi – ‘Yan bindiga sun kai mummunan hari gidan kwamishinan zabe a Lokoja da ke jihar Kogi.

Legit ta tattaro cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 3:30 na daren yau Juma’a 1 a watan Disamba.

'Yan bindiga sun kai hari kan gidan kwamishinan zabe
Mahara sun kai farmaki gidan kwamishinan zaben jihar Kogi. Hoto: INEC Nigeria.
Asali: Facebook

A ina maharan su ka kai hari?

Kara karanta wannan

Luguden wuta: An kashe yan bindiga sama da 50 yayin da suka kai hari a jihar arewa

Hukumar zabe mai zaman kanta, INEC ta bayyana wannan mummunan labari a shafukan sada zumunta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

INEC ta ce maharan ma su dauke da muggan makamai sun farmaki jami’an tsaron da ke wurin inda su ka yi artabu har na tsawon mintuna 30.

Rahotanni sun tabbatar da cewa ba a samu rasa rayuka ba yayin wannan mummunan hari da aka kai.

Wane martani INEC ta yi kan harin?

Sanarwar hukumar INEC ta ce:

“An yi asarar dukiyoyi yayin artabun tsakanin jami’an tsaro da kuma ‘yan bindigan a jihar Kogi.
“Gungun jami’an tsaro sun isa wurin don kare rayukan mutane, wannan na zuwa ne bayan jama’a sun mamaye ofishinmu a jihar.
“Mu na kira da ayi kwakkwaran bincike don tabbatar da kare lafiyar ma’aikatanmu da kayayyakinmu a jihar Kogi.”

Wannan na zuwa ne makwanni kadan bayan kammala zaben jihar Kogi wanda dan takarar APC, Usman Ododo ya lashe zaben.

Kara karanta wannan

Yanzu: Tashin hankali yayin da jami'an NSCDC suka harbi dalibai a Abuja yayin jarrabawa

A zaben da aka gudanar a ranar 11 ga watan Nuwamba, dan takarar jam'iyyar APC Alhaji Usman Ododo shi ya lashe zaben a kuri'u mafi rinjaye.

Murtala Ajaka daga jam'iyyar SDP shi ya kasance na biyu yayin da Dino Melaye daga jami'yyar PDP ya biyo shi a baya a matsayin na uku.

Hatsarin jirgin ruwa ya yi ajalin wani soja

A wani labarin, wani mummunan hatsarin jirgin ruwa ya hallaka wani soja a jihar Ribas.

Hatsarin ya faru ne a karshen makon da ya gabata bayan igiyar ruwa ta yi jifa da jirgin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel